Kano: 'Yan Kasuwa Sun Tafka Asara Yayin da Ruwan Sama Ya Mamaye Kasuwar Kantin Kwari

Kano: 'Yan Kasuwa Sun Tafka Asara Yayin da Ruwan Sama Ya Mamaye Kasuwar Kantin Kwari

  • Gagarumar ambaliyar ruwa ta faru sakamakon mamakon ruwan sama da aka yi a ranakun Lahadi da Litinin a kwaryar birnin Kano
  • 'Yan kasuwar sutturu na Kantin Kwari na cigaba da kirga asara yayin da ambaliyar ruwa ta lalata kayan sama da N200 miliyan
  • An gano cewa, shaguna da rumfunan 'yan kasuwa sama da 250 ne suka salwanta inda ambaliyar ruwan har ofishin SEMA ta hada da

Kano - Masu sana'ar sutturu a fitacciyar kasuwar Kantin Kwari suna cigaba da kirga asara bayan gagarumar ambaliyar ruwa ta lalata kayan sama da N200 miliyan a sama da shaguna 250 da rumfuna.

Wannan ya faru ne sakamakon mamakon ruwan sama da aka yi a ranakun Lahadi da Litinin a kusan dukkan yankunan birnin Kano wanda ya kawo ambaliyar ruwa har a ofishin hukumar taimakon gaggawa ta jihar, SEMA.

Kara karanta wannan

Babban gaye: Yadda nau'in takalmin wani dan kwalisa ya girgiza mutane a intanet

Kantin Kwari
Kano: 'Yan Kasuwa Sun Tafka Asara Yayin da Ruwan Sama Ya Mamaye Kasuwar Kantin Kwari. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

An kwashe sama da sa'o'i hudu ana zabga ruwan sama a kwaryar birnin a ranar Litinin, Daily Trust ta lura cewa manyan tituna da wasu anguwanni duk sun cika makil da ruwa.

Wannan ya saba faruwa tun daga farkon daminar inda kusan dukkan magudanun ruwa ke toshewa da datti kuma a halin yanzu akwai gine-ginen da aka yi a hanyar ruwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daily Trust ta rahoto cewa, a farkon watan nan SEMA tace a kalla rayuka tara da gidaje 6,417 ne suka salwanta yayin da kadarorin sama da N500 miliyan suka salwanta tun daga farkon daminar bana.

'Yan kasuwa sun dora laifi a kan gwamnati kan gine-gine

Da yawan 'yan kasuwar Kantin Kwari sun dora laifin abinda ke faruwa a kan gwamnati wacce suka ce ta dinga gine-gine a kan hanyoyin ruwa da titunan kasuwar.

Kara karanta wannan

Washegarin Biki, Ango da 'Yan Biki 5 Sun Sheka Lahira, Wasu Suna Asibiti Rai a Hannun Allah

SEMA ta koka da rashin tsaftar 'yan kasuwan inda tace hakan ne ke kawo toshewar magudanun ruwa da suka rage a kasuwar.

Jerin sunayen jihohi 32 na Najeriya da za a fuskanci ambaliyar ruwa a 2022

A wani labari na daban, darakta janar na Nigeria Hydrological Services Agency, NIHSA, Clement Nze, ya ce bayanai daga binciken ambaliyar ruwa na shekarar 2022 sun nuna cewa za a samu ambaliyar ruwa a jihohi 32 na kasar nan har da babban birnin tarayya na Abuja.

A yayin jawabi a Abuja lokacin gabatar da kiyasin hukumar na wuraren da za a iya samun ambaliyar ruwa, ya bayyana jihohin Adamawa, Abia, Akwa Ibom, Anambra, Bauchi, Bayelsa, Benue, Cross-River, Delta, Ebonyi, Ekiti, Edo a cikin wuraren da ake kyautata tsammanin samun ambaliyar ruwan.

Har ila yau, sauran jihohin da ake kyautata zaton samun ambaliyar ruwan sun hada da Gombe, Imo, Jigawa, Kaduna, Kano, Kebbi, Kogi, Kwara, Legas, Nasarawa, Niger, Ogun, Ondo, Oyo, Rivers, Sokoto, Taraba, Zamfara da FCT Abuja.

Kara karanta wannan

Mutuwa ta yi raha: Yadda kasuwar makara da akwatin gawa ke ci a kasar Kamaru

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel