Yadda Kasuwar Akwatin Gawa Ke Ci a Kamaru Saboda Barkewar Yaki

Yadda Kasuwar Akwatin Gawa Ke Ci a Kamaru Saboda Barkewar Yaki

  • Akalla shekaru 5 aka kwashe ana gwabzawa a birnin Bamenda na jamhuriyar Kamaru, lamarin da ya sauya birnin zaman lafiya zuwa filin daga
  • Sakamakon kazamin yakin, birnin Bamenda ya zama yankin da ke ganin mace-mace, mazauna sun kama sana'ar siyar da akwatin gawa
  • Ana dai gwabza yakin ne tsakanin jama'a masu magana da turancin Ingilishi da kuma gwamnatin Faransanci a kasar

Bamenda, Kamaru - Wani birni mai cike da walwala a Kamaru mai suna Bamenda a yanzu ya zama mayanka da zangon mutuwa tun bayan barkewar yaki shekaru biyar da suka gabata.

BBC Pidgin ta ce, yakin ana tafka shi ne yana tsakanin masu tutiya da turancin Ingilishi da kuma gwamnatin Faransanci.

A yanzu dai a birnin Bamenda babu abin da ya fi ciniki fiye da makara da akwatin binne gawa saboda wurin ya zama zangon mutuwa.

Kara karanta wannan

Bacin rana: Wani ya yi aikin dana sani, ya kashe masoyiyarsa saboda katin ATM

Mutuwa ta zama araha a Kamaru, makara ta zama kayan kudi
Yadda kasuwar akwatin gawa ke ci a Kamara saboda barkewar yaki | Hoto: @bbcnewspidgin
Asali: Twitter

Wannan kuwa ya faru ne kasancewar yadda ake zubar da gawarwaki a garin barkatai a kowane lokaci.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

An ce ma'aikatan gwamnati na dauko gawarwaki daga dakin ajiyarsu, kan tituna da bakin koguna domin binne su ko ma ta wane hali ne.

Sai an yi sa'a a binne mutum

Wani ma'aikacin hukumar kula da makabarta da ya zanta da manema labarai ya ce, a yanzu ba karamar sa'a gawa za ta yi ta samu a binne ta ba.

Ya bayyana haka ne tare da cewa a yanzu haka ya siya wasu akwatun gawa guda 10 masu araha don aiwatar bison wasu mamata.

A cewarsa:

"Albarka ce idan ka samu aka binne ka ma gaba daya, ba ma wai batun a tara iyalai da danginka ba."

Bukatar akwati mai zane na musamman kamar Injila, mota da kwalaben giya wajen nuna irin rayuwar da mutumin ya yi, abin da yake sha'awa da fatansa karshe ya ragu.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An gano gawarwakin wasu adadi na mutanen da suka mutu a benen Abuja

A bangare guda, wani dillalin akwatin gawa ya ce akwati mai tsada a kasuwa ya kau saboda a yanzu dai babu bukatarsa.

A yanzu binne gawarwakin matasa da yara kanana a yankin masu tutiya da turancin Ingilishi ya zama ruwan dare kuma abin tunawa a yankin Arewa maso Gabas da Kudu maso Yammaci.

A cikin shekaru biyar kacal, dubun dubatar mutane ne suka rasa rayukansu a yakin, kuma akalla sama da mutane miliyan 1 ne suka rabu da gidajensu zuwa yankunan masu tutiya da Faransanci.

An ce akwai kuma kusan mutane 80,000 daga yankin da ke fake a Najeriya.

Mai ƙera akwatin gawa ya zama miloniya a dare guda bayan dutse daga sararin samaniya ya faɗo a gidansa

A wani labarin, wani bawan Allah ya zama miloniya cikin dare daya bayan wani dutse daga sararin samaniya ya fado gidansa bayan fasa rufin gidan.

Mutumin mai suna Josua Hutagalung dan asalin kasar Indonesia ya sayar da dutsen ga wani kwararren mai sayen kayayyaki kan £1.4 milliyan (N766 miliyan), The Sun ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Allahu Akbar: Daga samun mafaka a masallaci, dan Ukraine ya Musulunta

Lamarin ya faru ne a shekarar 2020 a wata rana da Josua ke zaune a gida. A lokacin da ya ji wani sauti mai ratsa kunne sakamakon fadowar dutsen, Josua ya yi ta tunanin shin menene ya fado duba da cewa ba ruwan sama ake yi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel