Manyan ayyuka 5 da gwamnati ta fara yiwa 'yan kasa, amma ta gaza karasawa
- A duk shekara, gwamnatin Najeriya na ba da manyan ayyuka daban-daban a fadin kasar nan da kuma amincewa da sakin biliyoyin Nairori domin yinsu
- Sai dai, abin bakin cikin shi ne, yawancin wadannan ayyukan ba a kammala su, da yawa akan yi watsi dasu ba tare da wani bayani ga 'yan kasa da ake wa aikin ba
- Duk da cewa akwai ayyuka birjik da ba kammala ba, amma akwai wadanda baki ba zai iya shuru ba sai an fada, saboda adadin kudaden da aka kashe a kansu
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Gwamnatocin Najeriya daban-daban ne suka fara ayyuka masu muhimmaci ga kasa, kuma hukumomi suka amince da kashe makudan biliyoyi domin ayyukan a tsawon shekaru.
An sanar da irin wadannan ayyukan ga talakawa, kuma hakan ya faranta musu, amma kuma aka bar su baki hangale saboda ba kammala ayyukan ba.
Abin takaicin ma shi ne, yawancin ayyukan da suke ga su birjik a Najeriya an fara su ne, amma kuma aka yi asarar kudin fara aiki da cin wuri amma ba gama ba. Talaka ya kalla ya ji haushi, ya tuna ransa ya sosu.
Ga dai biyar daga cikin wadannan ayyuka kamar haka:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Babban dakin karatu na kasa
- Kudin aikinsa: Naira biliyan 18
- Shekarar da aka fara: 2006
- Matakin aikin a yanzu: Bai kammala ba
Har yanzu ba a kammala ginin hedkwatar dakin karatu na Najeriya da ke Lamba 35 a babbar cibiyar kasuwanci ta Abuja.
Gwamnati ta ba kamfanin Messes Reynolds Development Company (RCC) ne kwangilar a 2006 kan Naira biliyan 8.590.
Sai dai, an dakatar da ginin saboda gazawar gwamnati wajen biyan kudaden da aka yarje za a biya na aikin. Dan kwangilar ya bukaci a kara masa kudi a 2008.
Bayan dogon batu, majalisar zartaswa ta tarayya (FEC), an kara kudin aikin zuwa Naira biliyan 18 a 2009 kuma aka sanya watan Yulin 2010 a matsayin lokacin da za a kammala, amma dai bata sauya zane ba.
Titin Apo-Karshi
- Kudin aikin: Naira biliyan 6.4
- Shekara da aka fara: 2011
- Matakin aikin a yanzu: Bai kammala ba
An amince da kashe Naira biliyan 6.4 na aikin titin Apo zuwa Karshi ga kamfanin Kakarta Engineering Limited.
A cewar hukumar babban birnin tarayya, an ba da aikin ne ganin yadda 'yan kasa suka sa gwamnati a gaba kan matsalolin hanya da masu ababen hawa ke fuskanta a kan hanyar AYA-Nyanya-Mararaba-Keffi.
Sai dai, a 2015, an dakatar da aikin bayan zabe, lamarin da ya sa har yanzu masu ababen hawa ke fama a hanyar. Har yanzu ba kammala aikin ba, amma gwamnati ta ce a kara hakuri.
Hasumiyar Millennium Tower
- Kudin aikin: Naira biliyan 69.3
- Shekarar da aka fara: 2005
- Matakin aikin a yanzu: Bai kammala ba
An fara gagarumin aikin ginin Millennium Tower, a 2005 a zamanin gwamnatin Olusegun Obasanjo.
An nufi gina hasumiya mafi tsayi a Abuja mai tsawon mita 170 (kafa 560) wanda za a kashe N69.3bn.
A watan Afrilun bana, gwamnatin Buhari ta masu zuba hannun jari masu zaman kansu da su zuba dala miliyan 400 don kammala wannan hasumiyar, inji rahoton PremuimTimes.
Ayyukan iskar gas da ba a kammala ba
- Kudin aikin: $9.8 ( an ba OK LNG)
- Shekarar da aka fara: 2005
- Matakin aikin a yanzu: Bai kammala ba
A wani bangaren, akwai wasu muhimman ayyuka biyu da aka bayar na iskar gas na Olokola Liquefied Natural Gas (OK LNG) da kuma West African Gas Pipeline (WAGP).
Ayyukan nan da aka nufi su habaka tattalin arzikin Najeriya ta fuskar iskar gas har yanzu ba su kammala ba duk da cinye Naira biliyan 64.96 tas a 2020 kuma babu alamar gas.
Hedkwatar ma'aikatar noma
- Kudin aikin: Naira biliyan 7.075
- Shekarar da aka fara: 2019
- Matakin aikin a yanzu: Bai kammala ba
Haka nan wannan aikin na hedkwatar ma'aikatar noma, har yanzu babu labari, talakawa na ci gaba da wanke hannu suna jira.
Ku Je Ku Ji da Batun Addini Ku Bar Hango Makomar Siyasa, Kakakin APC Ga Malamai
A wani labarin, zaben 2023 na zuwa, karamin ministan kwadago kuma kakakin gangamin kamfen na Tinubu, Festus Keyamo (SAN), ya shawarci fastoci da sauran malaman addini da su koyi darasi da abin da ya faru 2015.
Ya kuma kiraye su da su kaucewa sakin baki sakaka wajen tofin na iya hange da shiga hurumin ubangiji don burge mabiyansu.
Kayem ya fadi haka ne yayin wata tattaunawa ta musamman da jaridar Punch a Abuja, inda ya kuma shawarci malaman addini da su “fuskanci ainihin abin da suka sa a gaba”.
Asali: Legit.ng