Zamfara: A Dena Ɓata Lokaci, A Riƙa Aika Ƴan Bindiga Wurin Mahallicinsu, In Ji Shinkafi

Zamfara: A Dena Ɓata Lokaci, A Riƙa Aika Ƴan Bindiga Wurin Mahallicinsu, In Ji Shinkafi

  • Shugaban kwamitin sasanci da yan bindigan Zamfara, Abdullahi Shinkafi ya koka kan jinkiri da ake yi wurin hukunta yan bindiga
  • Shinkafi ya yi ikirarin cewa jami'an tsaro da alkalai da kuma lauyoyi ne suke bawa masu laifin kariya a maimakon a hukunta su cikin gaggawa
  • Shugaban kwamitin ya ce bai kamata a bata lokaci kan dogon bincike ba muddin an kama dan bindiga yana aikata laifi dumu-dumu kawai a aika shi zuwa ga mahallacinsa

Zamfara - Abdullahi Shinkafi, shugaban kwamitin sassanci da yan bindiga a Zamfara ya koka kan yadda ake tafiyar hawainiya wurin bincike da hukunta yan bindiga, rahoton Daily Trust.

Ya dora laifin hakan kan jami'an tsaro, alkalai da lauyoyi da ya yi ikirarin suna bawa masu laifin kariya.

Kara karanta wannan

Harin Jirgin kasa: 'Dan Uwan Budurwar da Shugaban Yan Bindiga Ke Kokarin Aurawa Kansa Ya Koka

Turji
Zamfara: A Dena Ɓata Lokaci, A Riƙa Aika Ƴan Bindiga Wurin Mahallicinsu, Shinkafi. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya yi wannan jawabin ne a ranar Talata bayan kwamitinsa ta yi taro kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Ya ce:

"Babban matsar da muke samu shine jami'an tsaro da alkalai da lauyoyi da ke kare masu laifin, idan ka kama yan bindiga da AK-47 11, wane hujja ka ke jira? Ya kamata a aika shi wurin mahallacinsa.
"Idan an kama dan bindiga dumu-dumu, yana kashe mutane kuma kana jiran bincike, mene ka ke bincikawa? Ka aika shi wurin mahallicinsa."

Ni ba zan sake sansanci da yan bindiga ba, Shinkafi

Abdullahi Shinkafi, ya ce kuma ce kwamitinsa ba za ta sake sasanci da wani dan bindiga ba domin mafi yawancinsu ba da gaske suke ba.

Kalamansa:

"A bangare na, na san ya rungumi zaman lafiya amma ba zan iya cewa ya tuba ba, sai ya mika wuya tare da dukkan bindigu da makamansa, ya zo gidan gwamnati ya mika makamansa kamar yadda sauran tubabbun yan bindiga suka yi.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Yan bindiga Sun Sako Kwamishanan Jihar Nasarawa

"Duk wani batun sasanci da yan bindiga, a cire ni daga ciki domin mafi yawancinsu ba da gaske suke yi ba, yaudaran mu suke, duk wani yarjejeniya da kuka yi da su, za su koma mummunar sana'arsu, mafi yawancin su."

Asali: Legit.ng

Online view pixel