Ku Je Ku Ji da Batun Addini Ku Bar Hango Makomar Siyasa, Kakakin APC Ga Malamai

Ku Je Ku Ji da Batun Addini Ku Bar Hango Makomar Siyasa, Kakakin APC Ga Malamai

  • Festus Keyamo, daya daga cikin ministocin Buhari ya ba da sako a ba fastocin Najeriya yayin da zaben 2023 ke gabatowa
  • A lokutan buga gangar siyasa a Satumban bana, Keyamo ya shawarci malaman addini su kau da kai ga harkokin siyasa, su kawai dukufa da hankali kan harkar su addini
  • Hakazalika, ya shawarci fastoci 'yan hange-hange da su kame harshe daga hasashen siyasa domin za su yi nadamar sakamakon zaben 2023

Zaben 2023 na zuwa, karamin ministan kwadago kuma kakakin gangamin kamfen na Tinubu, Festus Keyamo (SAN), ya shawarci fastoci da sauran malaman addini da su koyi darasi da abin da ya faru 2015.

Ya kuma kiraye su da su kaucewa sakin baki sakaka wajen tofin na iya hange da shiga hurumin ubangiji don burge mabiyansu.

Festus Kayemo ya caccaki malamai, ya ce su kama addini su bar siyasa
Ku Je Ku Ji da Batun Addini Ku Bar Hango Makomar Siyasa, Kakakin APC Ga Malamai | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Kayem ya fadi haka ne yayin wata tattaunawa ta musamman da jaridar Punch a Abuja, inda ya kuma shawarci malaman addini da su “fuskanci ainihin abin da suka sa a gaba”.

Kara karanta wannan

Aljannar Duniya: Bidiyon Katafaren Jirgin Sama Mai Dauke Da Dakunan Barci 2 Ya Yadu A Soshiyal Midiya

Yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“A samu fastoci sun karkata ga wani dan takara da suke so abu ne mai kyau ga kasa amma fa bayan ya fadi, yanzu za ka sun koma ga ainihin aikinsu.
"Kuskure ne da suke tafkawa kuma abu nemai muhimmanci su yi hakan. Na yi tsammanin za su koyi darasi daga abin da ya faru a 2015 sai su raba batun coci da siyasa; amma sun kasa.
“Amfaninsu shi ne su kira mutane zuwa ga bin Allah ba wai zuwa ga (Fadar Shugaban kasa) Villa ba, Villa ba ta aljanna ba ce.
“Allah zai sa hakan ta faru a yanzu haka, domin bayan 2023, za fahimci kura-kuransu kuma cewa sun mai da coci wurin yin da bai kamata ba.”

Jaridar PM News ta ruwaito yana kuma cewa, shi kirista ne da ya imani da addini, amma yana da yakinin cewa Allah bai ba fastoci ilhamar hango wanda zai yi mulki ba.

Kara karanta wannan

Yajin ASUU: Farfesa Maqari ya tona asirin malaman jami'a, ya fallasa sirrin da suke boyewa

Ya kuma bayyana cewa, ba ma hurumin limamai da malamai bane su hasaso wanda Allah ya zaba ya bashi mulki.

Daga Karshe Dai Dan Takarar APC Tinubu Ya Bayyana Inda Yake Samo Kudi

A wani labarin, dan takarar shugaban kasa ajam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana gaskiyar sana'ar da yake yi kuma har ya tara dukiya mai yawa.

Tinubu ya yi nuni da cewa, duk wani wayayyen dan Najeriyan da kwashi kudinsa N1.8m kacal ya zuwa hannun jari a kamfanin Apple a 1980 to ya zuwa yanzu ya mallaki sama da Naira Tiriliyan 10.

A wani rubutu ta Facebook da Joe Igbokwe ya yada, Tinubu ya bayyana cewa ya mallaki miloniyoyin daloli akalla shekaru 10 kafin ya zama gwamnan jihar Legas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel