Jerin Gwamnonin Najeriya 8 Da Suka Kwancewa Sarakuna Rawani a Jihohinsu

Jerin Gwamnonin Najeriya 8 Da Suka Kwancewa Sarakuna Rawani a Jihohinsu

  • Kwancewa Sarakuna rawani wani abu ne da aka dade ana yi tun lokacin Sir Ahmadu Bello Sardauna
  • Tun dawowar Demokradiyya Najeriya, gwamnoni sun cire Sarakuna a jihohin bisa dalilai da dama
  • Sarakuna sama da goma aka kwance rawani tun da aka dawo da Demokradiyya a 1999

Kwancewa Sarkin gargajiya rawani a Najeriya abu ne wanda aka dade ana yi tun bayan samun yancin Najeriya daga hannun turawan mulkin mallaka.

Tun dawowar demokradiyya a 1999, sabani, rashin jituwa musamman na siyasa ya yi sanadin cire rawanin wasu Sarakuna a Arewa da Kudancin Najeriya.

Tare da TheNation, Mun tattaro muku jerin wasu gwamnoni a Najeriya da suka taba kwance rawani sarkin a zamaninsu

GWamnoni
Jerin Gwamnonin Najeriya Da Suka Kwancewa Sarakuna Rawani a Jihohinsu Hoto: Wike, Ganduje, Matawalle, Mimiko
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Bayan Kwanaki 30 a Tsare, An Sako Shahrarren Lauya Daga Kurkuku

Na baya-bayan nan shine Gwamna Kano, Abdullahi Umar Ganduje, wanda ya tsige Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu.

Kundin tsarin mulkin Najeriya ya baiwa gwamnoni karfin tsige Sarki a Najeriya.

Ga jerin gwamnonin da suka cire Sarakuna:

1. Bello Matawalle, Zamfara, 2022

Gwamna Matawalle ya cire Sarkin Zurmi, Abubakar Atiku, Sarkin Dansadau, Hussaini Umar, da Sulaiman Ibrahim, Dagacin Birnin Tsaba bisa zargin hada kai da yan bindiga

2. Abdullahi Ganduje, Kano, 2020

Gwamna Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya tsige Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu bisa zargin shiga harkar siyasa

3. Willie Obiano, Anambra 2020

Ya tsige Igwe Chijioke Nwankwo of Nawfia, Igwe Anthony Onyekwere of Owelle da Igwe G. B. C. Mbakwe of Abacha.

4. Nyeson Wike, Rivers, 2019

Ya tsige Sarkin Baabe

5. Olusegun Mimiko, Ondo, 2010

Ya tsige Deji of Akure of Akure Oba Oluwadamilare Adesina Osupa III bisa dukkan matarsa a cikin fada

Kara karanta wannan

Atiku ya kade: Obasanjo ya gana da Peter Obi, Wike da wasu jiga-jigai a Landan

6. Adams Oshiomhole, Edo, 2016

Ya tsige Anslem Aidenojie (Onojie of Uromi) bisa zagin wata mata kuma ya ki bada hakuri. Amma daga baya Gwamna Godwin Obaseki ya mayar da shi

7. Martin Elechi, Ebonyi, 2013

Ya tsige Eze Joseph Oko. Ivi of Akaeze bisa yawan shan giyansa yayinda ya tsoge Eze Micheal Orji bisa adawa da gwamnati.

8. Muhammad Adamu Aliero, Kebbi, 2005

Ya tsige Sarkin Gwandu Mustapha Jokolo bisa kalaman da basu dace ba

Asali: Legit.ng

Online view pixel