Yara da basu wuci shekaru biyar da haihuwa ba na fuskantar barazanar mace-mace a Najeriya

Yara da basu wuci shekaru biyar da haihuwa ba na fuskantar barazanar mace-mace a Najeriya

Adadin yara masu fuskantar barazanar mace-mace kafin su cika shekaru biyar da haihuwa yana hauhawa kamar yadda bincike na Multiple Indicator Cluster Survey, MICS ya bayyanar.

A jawaban ta na wani taron kwanaki biyu da majalisar ɗinkin duniya reshen kula ƙananan yara ta gudanar, Maureen Zubie-Okoro jagorar binciken ta bayyana cewa, Najeriya tana kan gaba cikin jerin ƙasashen da suke kere sauran wajen adadin yara da ke mutuwa kafin su cika shekaru biyar na rayuwarsu.

Hoton ƙananan yara
Hoton ƙananan yara
Asali: UGC

Kwararrar ta kuma bayyana cewa, duk da cewar an samu raguwar wannan adadin daga 97 zuwa 70 cikin kowace haihuwa 1000 a binciken da cibiyar MICS ta fitar a shekarar 2011, a yanzu adadin ya ƙara linkuwa domin kuwa cikin ko wace haihuwa 10 akwai 1 da take salwanta kafin cikar ta shekaru 5 da haihuw.

KARANTA KUMA: Kasar Rasha ta kausasa harshe akan shugaban ƙasar Amurka Donald Trump

Maureen ta ƙara da cewa, Najeriya ce ƙasa ta uku a duniya da suke fuskantar wannan barazana, inda ƙasashen Nijar da kuma Senegal suke a sahu na farko.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng