Yadda Dogarin Minista Ya Lakadi Ma'aikata da 'Dan Jarida a Gidan Buhari

Yadda Dogarin Minista Ya Lakadi Ma'aikata da 'Dan Jarida a Gidan Buhari

  • Dogarin karamar minista Ramatu Tijjani Aliyu, ya tsinke mataimakin kwamishinan 'yan sandan da mari a gidan Buhari
  • An gano cewa, lamarin ya faru ne bayan 'yan sanda basu budewa uwardakinsa get din fita ba bayan ta kammala taro da kungiyoyin mata a sakateriyar
  • Tuni jami'an 'yan sandan dake wurin suka lakada masa duka har da fashe masa kai sannan suka nemi far wa 'dan jaridar dake wurin da duka

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT, Abuja - Dogarin karamar ministan babban birnin tarayya, Ramatu Tijjani Aliyu a yammacin Alhamis ya lakadi jami'an tsaro da mai daukar hoto a gidan Buhari dake sakateriyar jam'iyyar APC ta kasa bayan hayaniyar da ta hada shi da jami'an tsaron kofar shiga sakateriyar.

Aliyu ita ce shugaban mata ta jam'iyyar APC a lokacin da John Oyegun ke jagorantar NWC kafin a nada ta minista, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Dan kasuwa ya toshe al'aurarsa saboda bai san ya sake haihuwa saboda tsadar kudin makaranta 'yayansa 5

Bayan kammala aikin gyaran sakateriyan, jami'an tsaro suna shan wahalar gyara zaman motoci a ma'adanarsu inda tawagar 'yan siyasa ke jera su.

Lamarin ya fara ne wurin karfe 6 na dare lokacin da ministar wacce ta kwashe kusan sa'a daya tana taro da kungiyoyin mata a sakateriyar ta shirya barin farfajiyar.

A maimakon jami'an tsaron sakateriyar su cire shingen kan hanyar fita, daya daga cikin dogaranta ya garzaya da gudu inda ya nemi saka karfi wurin cire shingen.

"Shugaban jami'an tsaron ofishin jam'iyyar, CSP ya bukacesa da ya jinkirta zuwa lokacin da jami'ansu zasu cire shingen. Babu bata lokaci jami'in tsaron ministan ya tsinke 'dan sandan da mari inda ya bukaci jin dalilin da yasa suka yi jjnkirin cire shingen bayan sun ga ministar na kokarin fitowa," wani jami'i da ya ga lokacin da lamarin ya faru ya bayyana.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Kwanan Nan Zamu Bayyana Sunayen Manyan Mutanen Dake Satar Mai, Fadar Shugaban Kasa

Yace sauran jami'an tsaro a sakateriyar sun kama dogarin ministan inda suka dinga dukansa har kan shi ya fashe.

"Bayan ganin abinda ke faruwa, sauran jami'an tsaron dake tawagar ministan sun sauka domin tarewa dogarin yayin da ministar ta zauna a motarta hankali kwance.
"Sun kara da lallasa mai daukar hoto wanda ke kokarin nadar lamarin da wayarsa amma bayyanar 'yan jarida biyu yasa suka hakura. An gaggauta sanya dogarin ministan a mota inda suka hanzarta barin farfajiyar," yace.

Duk da jam'iyyar har yanzu bata yi martani kan lamarin ba, wani jam'in gudanarwa na FCT yace babu laifin ministan.

Yace:

"Jami'an tsaron sakateriya kawai sun so batawa ministan suna ne. Ta fito waje ta tarar da jama'a aka ce mata mutane suna kokarin karbar kudin da ake rabawa ne a waje.
"Ta shige motarta tayi gaba. Daga bisani ne muka ji cewa rikici aka yi wanda har ta kai ga an fasawa jami'in tsaro kai.

Kara karanta wannan

Harin Jirgin kasa: 'Dan Uwan Budurwar da Shugaban Yan Bindiga Ke Kokarin Aurawa Kansa Ya Koka

"Batun shi ne, an ci zarafin ministan kuma jami'an tsaron sakateriyar suka je har da kai kara wurin 'yan sanda. Wannan ya biyo bayan hana mu kai korafi da ministar tayi."

Asali: Legit.ng

Online view pixel