Hotona da Bidiyoyin Bikin Zagayowar Ranar Haihuwar Amaryar Sanusi Lamido
- Amaryar tsohon sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II, ta yi bikin zagayowar ranar haihuwarta
- An gabatar da wani dan takaitaccen liyafa a cikin gida domin taya Gimbiya Sa'adamu Mustapha-Barkindo murnar wannan rana
- Tsohon sarkin, wasu daga cikin yaransu da uwargidarsa, Hajiya Sadiya Ado Bayero sun bayyana a bidiyo da hotunan shagalin
Najeriya - Sa’adatu Barkindo Sanusi, amaryar tsohon Sarkin Kano da aka tunbuke, Malam Muhammadu Sanusi II, ta yi bikin zagayowar ranar haihuwarta.
An shiryawa amaryar dan kwarya-kwaryan liyafa a gida wanda ya samu halartan tsohon sarkin da wasu daga cikin iyalinsa.
A cikin hotuna da bidiyon da suka yadu a soshiyal midiya, an gano mai martaba Sanusi II da Gimbiya Goggo Sasa tare da diyarsu yayin da suke yanka kek din da aka yi don wannan taro.
Uwargida Sarautar Mata: Kyawawan Hotunan Ministan Shari’a, Abubakar Malami Tare Da Matarsa, Fatima Malami
A wani hoton kuma, an gano su tare da dan tsohon sarkin namiji da kuma daya daga cikin manyan yaransa mata wato Fulani Siddika.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Haka kuma uwargidar Sanusi, Hajiya Sadiya Ado Bayero ta bayyana a cikin hotunan bikin zagayowar haihuwar kishiyar tata.
Goggo Sasa dai ita ce karama kuma ta hudu a cikin matan tsohon sarkin na Kano sannan ta kasance diya a wajen Lamidon Adamawa, Alhaji Musatapha-Barkindo.
Ga hotuna da bidiyoyin shagalin a kasa:
Jama'a sunyi martani
real__essential__north ta ce:
"Barka da zagayowar ranar haihuwarki ❤️."
muhammadbarudishehu ya yi martani:
"Sarki daya da ke arewa."
bazawara_in_arewa ta ce:
" MashaAllah."
aishajb26 ta ce:
"Maza irin SLS."
Bidiyon Bikin Zagayowar Ranar Haihuwar Tsohon Sarkin Kano, Sanusi, An Yanka Kek
A wani labarin kuma, mun kawo a baya cewa bidiyon bikin zagayowar ranar haihuwar tsohon sarkin Kano, Muhammad Sanusi Lamido ya bayyana a shafukan soshiyal midiya.
A ranar Lahadi, 31 ga watan Yuli ne Sanusi II ya cika shekaru 61 a duniya inda aka yi shagali na musamman domin raya wannan rana.
Sannan a gabansa wasu kek ne uku wadanda aka tanada saboda wannan shagali suna walwali. An kuma jiyo mutane suna rera masa wakar bazdai.
Asali: Legit.ng