Bidiyo da hotunan iyalan Sule Lamido a auren Surayya da Angonta Yazid Danfulani

Bidiyo da hotunan iyalan Sule Lamido a auren Surayya da Angonta Yazid Danfulani

  • Hotunan yan uwa da abokan arziki tare da iyalan tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido yayin da ya aurar da kyakyawar diyarsa
  • Kamar yadda bidiyo da hotuna suka bayyana, an ga mahaifin amaryar tare da kyakyawar amaryar inda ta yi shigar alfarma ta amaren zamani
  • Surayya Sule Lamido ta amarce da kwamishinan kasuwanci na jihar Zamfara, Yazid Danfulani a kayataccen bikin da aka yi a ranakun karshen makon nan

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jigawa - Kyawawan hotuna da bidiyoyin shagalin auren Surayya Sule Lamido da kyakyawan angonta Yazid Danfulani, kwamishinan kasuwanci na jihar Zamfara, sun bayyana.

Hotunan iyalan tsohon gwamnan jihar Jigawan, yan uwa da abokan arziki duk sun halarci wurin daurin auren, fashionseriesng suka wallafa a shafinsu na Instagram.

A shagalin da aka yi na bikin yar gatan ya dauka kala inda aka ganta da angonta, mahaifinta, mahaifiyarta da sauran yan uwa.

Kara karanta wannan

Kyakkyawar Diyar Tsohon Zababben Gwamnan Zamfara Ta Shiga Daga Ciki, Ya Yi Mata Kyautar Dankareriyar Sarka A Bidiyo

Surayya Sule Lamido
Bidiyo da hotunan iyalan Sule Lamido a auren Surayya da Angonta Yazid Danfulani. Hoto daga @fashionseriesng
Asali: Instagram

Daga cikin hotuna bidiyoyin da aka gani, an ga tsohon gwamnan tare da amaryar inda yake kallon diyarsa cike da kauna da soyayya yayin da ta yi shigar alfarma ta amaren zamani.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A wani bidiyo kuwa, an ga tsohon gwamnan a cikin shigar babbar riga a wurin daurin aure yana gaisawa da yan uwa da abokansa na arziki suna taya shi murna kan auran diyarsa.

Hotuna da Bidiyoyi: Shigar alfarmar da Surayya Sule Lamido Tayi a Liyafar Jajiberin Aurenta ya Kayatar

A wani labari na daban, biki yayi biki kuma shagali ya kankama yayin da Surayya Sule Lamido ke shirin amarcewa da angonta Yazid, kwamishinan kasuwani na Zamfara a cikin kwanakin nan.

Kamar yadda hotunan shagalin suka fara nunawa, an fara ne da fitar da hotunan kafin biki, hotuna da bidiyoyin sanya lalle suka biyo baya sannan hotuna da bidiyoyin liyafar cin abincin dare suka fito.

Kara karanta wannan

Bidiyon Bikin Dan Sanata Ahmed Sani Yariman Bakura Da Zukekiyar Amaryarsa Yar Kasar Waje, An Sanya Masa Lalle

A hotuna da bidiyoyin da Legit.ng ta tattaro na liyafar cin abincin daren, kyakyawar amaryar ta bayyana cike da shigar alfarma da kasaita wacce ta dace da tsarinta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Online view pixel