Bidiyon Bikin Zagayowar Ranar Haihuwar Tsohon Sarkin Kano, Sanusi, An Yanka Kek

Bidiyon Bikin Zagayowar Ranar Haihuwar Tsohon Sarkin Kano, Sanusi, An Yanka Kek

  • A ranar Lahadi, 31 ga watan Yuli ne tsohon sarkin Kano, Muhammad Sanusi Lamido, ya yi bikin zagayowar ranar haihuwarsa
  • Bidiyon shagalin ya yadu a Instagram inda Sanusi wanda ya cika shekaru 61 a duniya ya yanka kek
  • Jama'a sun taya sa murnar zagayowar wannan rana yayin da wasu suke ganin cewa a matsayinsa na Khalifa bai kamata ya yi wannan shagali ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Bidiyon bikin zagayowar ranar haihuwar tsohon sarkin Kano, Muhammad Sanusi Lamido ya bayyana a shafukan soshiyal midiya.

A ranar Lahadi, 31 ga watan Yuli ne Sanusi II ya cika shekaru 61 a duniya inda aka yi shagali na musamman domin raya wannan rana.

Sanusi
Bidiyon Bikin Zagayowar Ranar Haihuwar Tsohon Sarkin Kano, Sanusi, An Yanka Kek Hoto: shayheels
Asali: Instagram

A cikin bidiyon shagalin wanda shafin hausaa_fulanii ya wallafa a Instagram, an gano tsohon sarkin wanda ake yiwa lakabi da Dawisu sarkin ado tsaye cikin ado da kwalliya.

Kara karanta wannan

An Sha Fama: Bidiyon Yadda Wani Ango Ya Yi Sujjada Tare Da Fashewa Da Kuka A Wajen Daurin Aurensa

Sannan a gabansa wasu kek ne uku wadanda aka tanada saboda wannan shagali suna walwali. An kuma jiyo mutane suna rera masa wakar bazdai.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

khadijahasan8 ta yi martani:

"Mashaallah allah karawa sarki lafiya"

arc_aishadaraja ta rubuta:

"Khalifan khalifan ne.... ashe manyanmu na bazday? Rai ya kai da lfy da wadata ameen."

hbausa70 ya ce:

"Wannan shine tinkaho da addini."

musbahu_munir_matawalle ya yi martani:

"Kai Ina kataba ganin Khalifa yana birthday. Allah ya kyauta."

zahra_maiborno ta ce:

"Ran sarki ya dade ❣️"

Bidiyon Yadda Wani Ango Ya Yi Sujjada Tare Da Fashewa Da Kuka A Wajen Daurin Aurensa

A wani labarin, ranar aure rana ce ta farin ciki ga ango da amarya domin ganin cewa mafarkinsu na son kasancewa tare ya zama gaskiya.

Kuma kowani bawa na da yadda yake nuna farin cikinsa, wani kan yi dariya idan wata ni’ima ta same shi yayin da wani kuma kan zubar da hawaye don nuna farin cikinsa.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Ana Tsaka Da Ruwan Sama, Tsoho Ya Rikewa Matarsa Lema Cike Da Kauna

Hakan ce ta kasance a bangaren wani ango da bidiyonsa ya yada a shafukan soshiyal midiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel