Wani Uba Ya Damu da Yadda Dansa Yake Hana Shi Jin Dadin Aure da Matarsa

Wani Uba Ya Damu da Yadda Dansa Yake Hana Shi Jin Dadin Aure da Matarsa

  • Wani uban dan Najeriya ya koka kan halayyar dansa da ya hana shi sakat ya ji dadin rayuwar aure da matarsa
  • A cewar mahaifin, dan nasa baya barinsa sakat ya kulla alaka da matarsa domin ya kasance yana manne da ita kullum
  • Mutumin ya yada wani faifan bidiyo don tabbatar da maganarsa wannan yasa ‘yan Najeriya da dama suka tausaya masa kan halin da yake ciki

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Wani uba dan Najeriya ya yada bidiyon karamin dansa, Orji, wanda a duk lokacin da ya so zama da matarsa sai ya kawo masa tasgaro.

Da yake yada abin da yake faruwa dashi a TikTok, ya bayyana cewa tun lokacin da ya haifi dan nasa, yana da wahala ya samu dan lokaci shi kadai da matarsa su kebance.

Yadda yaro ke hana uwa da ubansa jin dadin rayuwarsu
Wani Uba Ya Damu da Yadda Dansa Yake Hana Shi Jin Dadin Aure da Matarsa | Hoto: TikTok/@orji4dad
Asali: UGC

Don tabbatar da labarinsa, ya daura wani bidiyo a TikTok wanda ya nuna dan nasa yana manne da mahaifiyar kuma ya ki barin gefenta.

Kara karanta wannan

Matashi Ya Sha Mamaki Bayan Ya Gano 'Yar TikTok Ta Yi Amfani Da Hotonsa Matsayin Marigayin Kawunta

Mahaifin mai suna Orij4dad a TikTok ya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Don Allah ban sani ba ko wannan lamari yana faruwa da duk masu aure da suka haihu. Tunda na haifi wannan yaron, duk lokacin da ke son ganin matata, yaron nan yana biye dani."

Kalli bidiyon:

Martanin 'yan TikTok

@mufasamoney__ yace:

"Daukarsa za ka yi ka kai shi gidan marayu, idan ya ga 'yan uwansa a can idan ya dawo zai natsu.

@uzzynwa4real ya rubuta:

"Yadda za mu warware wannan al'amari shi ne mu auro wa Orji wata mata kawai."

@alaba0421 yace:

"Uwa ce kashin bayan kowane yaro dan uwana kar ka yarda fa."

@temitayorebecca5 yace:

"Ba ka ma ga komai basai ka haifi 'ya'yan da za su kishiyanceka da mamansu oo......suna da kyau dai kam."

@edna22ng ta ce:

"Ina fuskantar matsala irin wannan a aurena ba zan taba iya zama da mijina ni kadai ba."

Kara karanta wannan

Musa Sani: Dan Najeriya Mai Shekaru 13 Ya Sake Kera Wata Gadar Sama, Hotunan Sun Yadu

@honeypot023 ya kara da cewa:

"Na farko dai ta yaya za ka sanya yaro suna Orji. Sunan manya."

Bidiyon Yaro Karami Na Tuka Mota a Hanya Ya Bar Jama’ar Intanet Baki Bude

A wani labarin, bidiyon wani karamin yaro da ke tuka mota da kansa kamar wanda ya kai shekarun da shari’a ta gindaya ya sa mutane da dama magana a intanet.

Wani mutumin da ya ga yaron yana murza matuki ya shiga mamaki kuma ya tambayi wanda ya ba shi motar.

Yaron dai ya ya amsa cikin murya kasa-kasa, duk da cewa ba a ji me yace ba. A cikin faifan bidiyon da aka yada a TikTok, an ga yaron yana juya sitiyari yana tafiya kamar kwararren direba, abin da ya ba masu kallo mamaki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel