Matashi Dan Shekaru 27 Zai Yi Wuff Da Budurwarsa Mai Shekaru 74 Wacce Ke Tuna Masa Da Kakarsa

Matashi Dan Shekaru 27 Zai Yi Wuff Da Budurwarsa Mai Shekaru 74 Wacce Ke Tuna Masa Da Kakarsa

  • Soyayya gamuwar jini domin ita ce ta hada wani matashi dan shekaru 27 da masoyiyarsa mai shekaru 74
  • Alaka ta yi nisa tsakanin Kathi Jenkins da Devaughn Aubrey domin har sun yi baiko kuma ana gab da daura masu aure
  • Matshin ya ce Kathi na tuna masa da kakarsa kuma tun ranar da suka hadu ya san cewa ita din burin zuciyarsa ce

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Texas - Wasu masoya wadanda suka hadu a shafin soshiyal midiya sun bayyanawa duniya irin son da suke yiwa junansu.

Kathi Jenkins mai shekaru 74 ta hadu da Devaughn Aubrey mai shekaru 27 inda suka yi zurfi a soyayya kuma a yanzu haka, masoyan wadanda suka fito daga Texas sun yi baiko kuma za su shiga daga ciki.

Kasancewar sun shafe tsawon shekara fiye da daya a soyayya, Devaugh ya ce ya san tsohuwar mai shekaru 74 ita ce burin ransa, shafin LIB ya rahoto.

Kara karanta wannan

Matashi Ya Sha Mamaki Bayan Ya Gano 'Yar TikTok Ta Yi Amfani Da Hotonsa Matsayin Marigayin Kawunta

Masoya
Matashi Dan Shekaru 27 Zai Yi Wuff Da Budurwarsa Mai Shekaru 74 Wacce Ke Tuna Masa Da Kakarsa Hoto: LIB
Asali: UGC

Ya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Mun hadu a yanar gizo. A wani shafin kulla halaka kuma dukkanmu ba wai mun je da zumar yin soyayya ta gaskiya bane.
“Hotonta ya ja hankalina. Na karanta bayananta sannan na aika mata da sako da nufin samun martani, itama tana kan layi sannan ta amsa sakon.
“Na tambayeta lambar wayanta sannan ta bani sai kuma ta tambaye ni yaya girman mambana inda muka dan zanta a wannan daren.”

Daga nan sai masoyan suka fara magana tsawon watanni hudu kafin haduwarsu, domin tafiyar awa biyu ne tsakaninsa da Kathi.

Devaughn ya ce a ranar da suka hadu tayi masa kyakkyawar tarba kuma sai ya ga ta fi haduwa sosai a zahiri.

Kathi ta yi soyayya da dama a baya amma bata taba aure ba. A yanzu haka tana da yara hudu, jikoki 13 da tattaba kunne 36 da kuma dan tattaba kunne daya.

Kara karanta wannan

Tare Da Ita Muka Sha Gwagwarmayar Rayuwa: Bidiyon Yadda Magidanci Ya Canza Rayuwar Matarsa

Devaughn wanda ke aiki a wani shago a Walmart bai da haihuwa amma ya taba aure a lokacin da yake da shekaru 24. Sai dai kuma sun rabu da matarsa a 2021 yan watanni kafin haduwarsu da Kathi. Ya kuma bayyana cewa wannan soyayya da ya shiga ba kamar na baya bane.

Ya ce tsawon lokacin da suka kwashe basu taba fada kuma ta yarda da shi sosai. Haka kuma ya ce tana rera masa wakoki masu dadi inda take tuna masa da kakarsa.

Komai Ya Ji: Bidiyoyin Wata Zukekekiyar Amarya Da Angonta Sun Haddasa Cece-kuce, Sun Hadu Matuka

A wani labarin kuma, jama’a sun yamutsa gashin baki bayan bayyanar bidiyon wata zukekiyar amarya da angonta a wajen liyafar bikinsu.

Tuni dai jama’a suka nadawa wannan amarya kambun ‘amaryar mako’ domin dai komai ya ji zam a bangarenta.

A cikin bidiyon da ya yadu a soshiyal midiya, an gano amaryar sanye da doguwar riga irin ta zamani yayinda angonta ya sanya farar shadda dinkin babban riga.

Kara karanta wannan

Soyayya Ruwan Zuma Dadi: Bidiyon Bature da Masoyiyarsa Bakar Fata Sune Holewa A Bakin Hanya

Asali: Legit.ng

Online view pixel