NSCDC Ta Ki karbar Cin Hancin Miliyan N10m, Yayin Da Ta kama Wani Shugaban Barayi a Sokoto

NSCDC Ta Ki karbar Cin Hancin Miliyan N10m, Yayin Da Ta kama Wani Shugaban Barayi a Sokoto

  • A karshen makon da ya gabata ne hukumar NSCDC ta gabatar da wasu gawurtattun yan bindiga guda biyu da suka kama a jihar Sokoto
  • Yan ta'adan da jami'an NSCDC suka kama sun yi yunkurin ba su cin hancin naira N10m domin a barsu su gudu
  • Yan Bidingan da jami'an NSCDC suka Kama a Sokoto sun addabi al’ummomi kananan hukumomin Silame, Binji, Gudu, Tureta da Dange/Shuni

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Sokoto - A karshen makon da ya gabata ne hukumar NSCDC a jihar Sokoto ta gabatar da wasu ‘yan bindiga guda biyu da suka addabi kananan hukumomin Silame, Binji, Gudu, Tureta da Dange/Shuni na jihar. Rahoton LEADERSHIP

Da yake jawabi ga manema labarai a hedikwatar rundunar NSCDC na Sokoto, kwamandan jihar, Muhammad Dada, ya ce Alhaji Koire da Alhaji Buba ’yan fashi ne masu hadari dake da yan bindiga sama da 300 a sansaninsu.

Kara karanta wannan

Antoni Janar Yayi Karin Haske Akan Hukuncin Yan kasuwar Canjin Kano da Ake Zargi Da Ba Boko Haram Kudi

Muhammad ya ce, su biyun sun addabi al’ummomi kananan hukumomin Silame, Binji, Gudu, Tureta da Dange/Shuni na jihar.

nscdc
NSCDC Ta Ki karbar Cin Hancin Miliyan N10m, Yayin Da Ta kama Wani Shugaban Barayi a Sokoto FOTO Legit.NG
Asali: Facebook

Manyan ‘yan bindiga dake gudanar da ayyukansu a Jamhuriyar Nijar da Najeriya musamman yankin Koire, sun tsere daga kamun jami’an tsaro ta hanyar amfani sihiri inji Mohammad.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mohammed yace a Lokacin da ya samu labarin inda suke a karamar hukumar Silame, shi da kanshi ya jagoranci mutanen sa kuma bayan kwashe kwanaki biyu a cikin daji suka yi nasarar kama su.

Bayan kama su, 'yan ta’addam suka yi yunkurin ba su cin hancin N10m domin a bar su su gudu.

A nasa jawabin, Alhaji Buba, ya ce yana da hannu wajen yin garkuwa da mutane a Dabegi da ke karamar hukumar Dange/ Shuni inda suka karbi kudin fansa naira miliyan hudu da kuma Kudula da ke karamar hukumar Gudu inda suka karbi kudin fansa naira miliyan daya.

Kara karanta wannan

Fitaccen lauya ga su Dangote: Ku taimaki ASUU kamar yadda kuka taimaka a lokacin Korona

Ya bayyana cewa suna da wani shugaba a jamhuriyar Nijar mai suna Danbuzu wanda ya kawo musu bindigogi kirar AK-47 da alburusai.

Harin Cocin Owo: MURIC Ta Nemi Biyan Diyya Ga Fulani Da Aka Kaiwa Hari

A wani labari kuma - Wata kungiyar kare hakkin bil’adama ta Musulunci MURIC, a ranar Alhamis ta yi kira da a biya diyya ga Fulanin da aka yi ramuwar gayya akan su bayan harin da aka kai wa masu ibada a cocin St. Francis Catholic Owo a Jihar Ondo.Rahoton Daily Trust

Legit.NG ta rawaito labarin yadda matasa suka kaiwa Fulani mazaunan garin Owo hari bisa zargin su suka kashe masu ibada cocin St. Francis.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Tofa avatar

Ibrahim Tofa

Online view pixel