Malami Yayi Bayani Akan Hukunta wadanda Aka Kama da Zargin Tallafawa Boko Haram Da Kudi

Malami Yayi Bayani Akan Hukunta wadanda Aka Kama da Zargin Tallafawa Boko Haram Da Kudi

  • Babban Lauyan Gwamantin Najeriya da Minsitan Sharia Abubakar Malami yayi bayyani Akan Hukunta wadanda aka Kama da Zargin tallafawa kungiyar Boko Haram Da Kudi
  • A shekarar da ta gabat ne gwamnatin tarayya ta sanar da kama wasu mutane da kuma kamfanonin dake samar wa Boko Haram Kudi
  • Abubakar Malami ya ce anyi nisa da bincike kuma har an saki wandanda aka gano ba su da hannu a cikin lamarin

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Babban Lauyan Gwamantin Najeriya da Minsitan Sharia Abubakar Malami, yayi bayyani Akan Hukunta wadanda aka Kama da Zargin tallafawa kungiyar Boko Haram Da Kudi. Rahoton BBC

A watan Fabrairun na shekara 2021 da ta gabata Gwamnati ta gano wasu mutane da kamfanoni kimanin dari daya dake agazawa mayakan kungiyar ISWAP tare da kama 45 daga cikinsu.

Kara karanta wannan

Fitaccen lauya ga su Dangote: Ku taimaki ASUU kamar yadda kuka taimaka a lokacin Korona

Bayan haka wasu bayyanan sirrin da hukumomin tsaro suka samu ya kai ga an kama yan canjin kudi kusan mutane 400 a jihohin 8 da suma ake zargin su da samar wa Boko Haram agajin kudi.

Malami
Malami Yayi Bayyani Akan Hukunta wadanda Aka Kama da Zargin Tallafawa Boko Haram Da Kudi FOTO LegitNG
Asali: Depositphotos

Sai dai a yayin da ‘yan Najeriya ke saka ayar tambaya kan yadda aka ji shiru na tsawon lokaci akan wannan batu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A wata hira da Babban Lauya kuma Ministan Shari’a na kasar Abubakar Malami yayi da BBC Hausa yace, tuni aka yi nisa da bincike kuma har an saki wandanda aka gano ba su da hannu a cikin lamarin.

Mun Kashe Triliyan N3.2 Da Muka Kwato Daga Barayin Gwamnati —Malami

A wani labari kuma, Abuja Babban Lauyan gwamnati kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, yace Najeriya ta kwato Naira triliyan 3.2 da aka sace daga kasar aka boye a bankuna daban-daban a duniya.Rahoton Aminiya

Abubakar Malami ya bayyana haka ne a lokacin da ya gana da yan jarida a Fadar shugaban kasa a ranar Alhamis.Ministan yace Ma’aikatarsa ce ta jagoranci kwato makudan kudaden daga shari’o’I a kasashen duniya a tsakanin watan Maris na shekara 2021 da watan Mayu na shekara 2022.

Asali: Legit.ng

Online view pixel