Jigawa: Yan Bindiga Sun Bude Wa Jami'an NIS Wuta, Sun Kashe Daya Sun Raunta Guda 2

Jigawa: Yan Bindiga Sun Bude Wa Jami'an NIS Wuta, Sun Kashe Daya Sun Raunta Guda 2

  • Wasu bata gari sun kai wa jami'an hukumar kula da shige da fice na kasa, NIS, hari a sansaninsu na sintiri a karamar hukumar Maigatari, Jihar Jigawa
  • Maharan sun taho a kan babura guda biyu ne suka kuma bude wa jami'an na NIS wuta, hakan yayi sanadin rasuwar jami'i daya da raunata wasu biyu
  • Jami'an na NIS sun mayar da martani nan take suka fatattaki yan bindigan cikin dajin Jamhuriyar Nijar suka kuma kwace baburansu biyu da wayan salula daya

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Jigawa - Yan bindiga a ranar Talata sun kashe jami'in hukumar shige da fice, NIS, guda daya sun kuma raunata wasu mutane biyu a karamar hukumar Maigatari a Jihar Jigawa, rahoton Premium Times.

Karamar hukumar Maigatari gari ne da ke da iyaka da Jamhuriyar Nijar.

Kara karanta wannan

Yadda Yan Bindiga Suka Farmaki Bikin Mutuwa, Suka Sace Masu Zaman Makoki Da Dafaffen Abinci

Jami'an Hukumar NIS
Yan Bindiga Sun Kashe Jami'in NIS, Run Raunata Wasu Biyu a Jigawa. Hoto: @PremiumTimesNg.
Asali: Twitter

Lamarin ya faru ne a kusa da garin Galadi-Birniwa, wanda ke da nisan kilomita 70 daga hedkwatar karamar hukumar.

Kwamandan hukumar NIS na Jihar Jigawa, Ismail Abba, ya shaidawa manema labarai cewa jami'ansa sun yi musayar wuta da yan bindigan hakan yasa suka tsere, Daily Nigerian ta rahoto.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Baburan da aka kwato.
Jigawa: Yan Bindiga Sun Bude Wa Jami'an NIS Wuta, Sun Kashe Daya Sun Raunta Guda 2. Hoto: @PremiumTimesNg.
Asali: Twitter

"Bata garin sun tsere cikin daji a Jamhuriyar Nijar sun bar baburansu biyu da wayan tarho."

Ya ce lamarin ya faru ne misalin karfe 11.20 na daren ranar Talata.

"Yan bindigan sun taho sansanin sintirin kan babura biyu, daya dauke da mutum uku dayan kuma dauke da mutum biyu, nan take suka bude wa ma'aikatan da ke bakin aiki wuta, hakan ya yi sanadin rasuwar ma'aikaci mai suna Abdullahi Mohammed.
"Wasu yan jami'an biyu sun samu munanan rauni na bindiga; sune Abba Musa Kiyawa da Zubairu Garba," Mr Abba ya kara da cewa.

Kara karanta wannan

Labari mai zafi: 'Yan bindiga sun hallaka Kodinetan hukumar FIRS, sun sace mutum 3

"Sakamakon musayar wutan, yan bindigan sun tsere cikin daji sun bar baburansu da wayar salula (Tecno T5)," in ji shi.

An kai gawar jami'in da ya rasu garin Dutse an masa jana'iza

Jami'an biyu da suka jikkata suna asibiti ana musu magani yayin da shi kuma Abdullahi Mohammed wanda ya rasu an masa jana'iza a ranar Laraba a garin Dutse.

Mr Abba ya ce za a mika baburan da wayar salular da aka kwato ga kwamishinan yan sanda don zurfafa bincike.

Yan Bindiga Sun Kai Hari Ofishin Yan Sanda, Sun Bindige Jami'i Daya Har Lahira a Ondo

A wani rahoton, yan bindiga sun kashe jami'in dan sanda mai suna Temenu Boluwaji a wani harin da suka kai a caji ofis na Okuta Elerinla a Akure Jihar Ondo.

Yan bindigan sun kai hari caji ofishin a safiyar ranar Litinin, The Cable ta rahoto.

Da ya ke tabbatar da lamarin, kakakin yan sandan jihar, Odunlami Funmilayo, cikin wata sanarwa ya ce harsashi ta ratsa mamamcin yayin musayar wuta da yan bindigan.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari Gida-Gida, Sun Kashe Mutane Sun Sace Wasu Da Dama

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164