2023: Babban Jigon PDP Ya Jinjinawa Bola Tinubu, Ya tsokano ‘Yan adawan APC

2023: Babban Jigon PDP Ya Jinjinawa Bola Tinubu, Ya tsokano ‘Yan adawan APC

  • Tsohon Gwamnan jihar Enugu, Dr. Chimaroke Nnamani ya kare Bola Tinubu daga masu sukarsa
  • Chimaroke Nnamani yana ganin wautar ‘yan adawan da ke kamfe da halin lafiyar ‘dan takaran
  • Sanatan yace ba a taba yin Gwamna irin Tinubu ba, sai dai duk da haka ba zai zabe shi a 2023 ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Chimaroke Nnamani ya yabawa ‘dan takaran shugaban kasa na APC, Asiwaju Bola Tinubu, yana mai tir da masu sukarsa saboda halin lafiyarsa.

A wasu dogoyen bayanai da ya yi a shafin Twitter a ranar 10 ga watan Agusta 2022, Chimaroke Nnamani yace ba a taba yin gwamna irin Bola Tinubu ba.

Sanatan na gabashin Enugu ya bada labarin irin rawar da Tinubu ya taka a lokacin yana gwamnan Legas, a lokacin Nnamani yana Gwamna a jihar Enugu.

Kara karanta wannan

Yajin Aikin ASUU: Ba Dole Ne Sai Kowa Ya Yi Digiri Ba, In Ji Gwamnan APC

Nnamani yake cewa Tinubu ya kawo tsare-tsaren da suka taimaka ya gyara harkar shari’a, ilmi, kiwon lafiya, kuma yayi aiki da wadanda ba Legasawa ba.

Premium Times ta kawo wannan rahoto inda aka ji tsohon gwamnan na PDP yana cewa duk Najeriya babu ‘dan siyasar da ya horas da mutane irin Tinubu.

Duk a shafin na sa, Nnamani ya yi bayanin yadda gwamnatin Tinubu ta samawa mutane ayyuka, sannan ta inganta harkar ilmi, aka bar gidaje da tituna.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Chimaroke Nnamani
Sanata Chimaroke Nnamani a Majalisa Hoto: @ChimarokeNamani
Asali: Twitter

Tattali ya bunkasa a lokacin Tinubu

A lokacin Tinubu yana gwamna, kudin shigan Legas a wata bai wuce N600m ba, amma kafin ya bar mulki, sai da jiha ta koma tatsar fiye da N8bn a wata.

30% na karfin tattalin arzikin kasar nan daga Legas ne, tare da 65% na kamfanonin da ake da su, 80% na kasuwancin ketare, kuma jihar ta ke kawo 60% na VAT.

Kara karanta wannan

2023: Abubuwa 5 da za su taimakawa Peter Obi a kan Tinubu, Atiku da Kwankwaso

Cuta ba mutuwa

Baya ga haka, tsohon gwamnan ya yi martani ga masu amfani da halin lafiyar Tinubu wajen cin ma burin siyasa, yace yin hakan sakarci ne da kuma jahilci.

Legit.ng Hausa ta ji yadda Nnamani a matsayinsa na Likita ya kawo misalan marasa lafiya wanda suka yi mulki a kasashen Duniya, kuma suka iya kawo cigaba.

Duk da irin yabon da kwararren Likitan da ya koma ‘dan siyasa ya yi wa ‘dan takaran na APC, ya ba shi shawarar ya ja kunnen mai dakinsa a kan sukar Inyamurai.

Ko da ya kwararo yabo ga Bola Tinubu, Sanatan yace kuri’arsa ta Atiku Abubakar ce a 2023. Hakan ya yi wa APC dadi, amma ya fusata magoya bayan PDP da LP.

LP za ta bada mamaki?

Mun kawo rahoto cewa alamu na nuna ‘Dan takaran na LP zai iya bada mamaki saboda wasu dalilai da suka shafi ra’ayin addini da daukar hankalin matasa.

Kara karanta wannan

Tinubu na kawai karfe 4 na dare bai yi barci ba yana aiki saboda tsananin kwazonsa , Shugaban matasan APC Dayo Isarel

Obi zai gwabza da Asiwaju Bola Tinubu, Atiku Abubakar da Rabiu Kwankwaso a zaben Shugaban kasa da za ayi a shekarar 2023 da babu wanda zai iya yin hasashe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel