Da Zafi-Zafi: Sojin Sama Sun Sheke Dan Ta’addan da Ya Kitsa Kai Hari Kan Tawagar Buhari a Daura

Da Zafi-Zafi: Sojin Sama Sun Sheke Dan Ta’addan da Ya Kitsa Kai Hari Kan Tawagar Buhari a Daura

  • An kashe wani kasurgumin dan ta’adda mai suna Abdulkarim Faca-Faca da ake zargin da hannu a kitsa harin da aka kaiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari
  • Wasu 'yan ta'adda sun farmaki tawagar shugaban kasa a yayin da ya kai ziyarar babbar sallah a birnin Daura
  • Yankin Arewa masu Yammacin Najeriya na daga cikin yankunan da suka fi fama da hare-haren 'yan bindiga

Safana, jihar Katsina - An kashe shugaban ‘yan ta’adda, Abdulkarim Faca-Faca, wanda ke cikin wadanda suka kitsa harin da aka kai wa ayarin motocin shugaban kasa Muhammadu Buhari a Katsina.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa an kashe shi ne tare da ‘yan kungiyar sa guda 8 a ranar Asabar 6 ga watan Agustan 2022.

Kara karanta wannan

Dattawan Arewa Sun Yi Koka Akan Yadda Kisan Yan Arewa Ya Yawaita A Kudu

Majiyoyi sun ce, an kashe shi ne yayin wani farmaki da rundunar sojojin saman Najeriya ta kai wani samame kan maboyar ‘yan ta’addan a kauyen Marina da ke karamar hukumar Safana a Katsina.

An gano dan ta'addam da a farmaki tawagar Buhari, ya bakunci kiyama
Da zafi-zafi: Sojin sama sun sheke dan ta'addan da ya kitsa kai hari kan tawagar Buhari a Daura | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Wata majiya daga tushe ta ce 'yan ta'adda da dama sun samu raunukan harbin bindigogi, sai daia abin takaici sun yi nasarar tserewa. Ta kuma ce, a yayin wannan aikin, an lalata shanun da barayin suka sato.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dan majalisa mai wakiltar Safana a majalisar dokokin jihar Kaduna, Abduljalil Runka, shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin.

A cewar Runka:

“Gaskiya ne. Da yammacin ranar Asabar ne sojojin saman Najeriya suka kai samame yankin inda suka ci gaba da fatattaka har safiyar yau. An kashe Abdulkarim Faca-faca da yaransa takwas a harin. An binne su ne a Marina, garinsu da safiyar Lahadin nan.”

Kara karanta wannan

Ganduje zai cika alkawari, zai rattaba hannu domin rataye wanda ya kashe Hanifa

'Yan Ta'adda Sun Sheka Barzahu Yayin Wani Artabu da Sojoji A Jihar Borno

Mazajen Sojojin Najeriya sun yi nasarar daƙile harin wasu da ake zargim mayaƙan ƙungiyar ta'addanci ISWAP ne a garon Monguno, jihar Borno, arewa maso gabashin Najeriya.

The Cable ta tattaro cewa yan ta'addan sun shiga garin ne da misalin ƙarfe 8:30 na dare ranar Jummu'a tare da motocin yaƙi, Babura da muggan makamai, suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi.

Wani jami'in hukumar tattara bayanan sirri ya shaida wa Zagazola Makama, masani kuma mai sharhi kan harkokin tada ƙayar baya cewa Sojoji sun tarbi yan ta'addan, suka yi musayar wuta har karfe 11:30 na dare.

Rahoto ya nuna cewa a wannan artabu da dakarun sojin Najeriya ne da yawan yan ta'adda suka sheƙa barzahu, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Karfin hali: Dan sanda Ya Kashe Wasu ‘Yan Bindiga 2 da Suka Kai Hari Gidansa

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Atiku ya ba da Dino Malaye babban matsayi a tawagar kamfen dinsa

A wani labarin, an kashe wasu ‘yan bindiga biyu a ranar Alhamis yayin da suka kai hari a gidan wani sufeton ‘yan sanda a garin Orogwe garin da ke a karamar hukumar Owerri ta Yamma a jihar Imo, a kudu maso gabashin Najeriya.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Michael Abattam ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, amma bai bayyana sunan sufeton ‘yan sandan ba, Premium Times ta ruwaito.

Ya ce ‘yan bindigar sun tsallake shingen gidansa ne kana suka shiga harabar gidan inda suka lalata masa kofa, amma sufeton ‘yan sandan ya yi dauki ba dadi dasu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel