Hotuna Da Bidiyo Sun Bayyana Daga ‘Kunshin’ Fatima Shettima

Hotuna Da Bidiyo Sun Bayyana Daga ‘Kunshin’ Fatima Shettima

  • Kyawawan hotuna da bidiyo sun bayyana daga liyafar kunshi wato ‘Henna Party’ din Fatima Shettima
  • Amarya ta sanya doguwar riga irin na isassun amare yayin da kawayen ta suka yi anko iri daya gaba dayansu
  • A ranar Asabar, 30 ga watan Yuli ne za a daura auren Fatima Kashim Shettima da angonta Sadiq Ibrahim Bunu

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Maiduguri, jihar Borno - Saura kwana daya alkawari ya cika tsakanin Fatima Kashim Shettima da angonta Sadiq Ibrahim Bunu.

Za’a daura auren diyar tsohon gwamnan jihar Borno kuma dan takarar mataimakin shugaban kasar Najeriya, Kashim Shettima da dan tsohon ministan Abuja, Ibrahim Bunu a ranar Asabar, 30 ga watan Yuli.

Sai dai kuma, tun a makon jiya ne aka fara shagalin bikin inda aka yi dina wanda ya samu halartan manyan masu fada aji a kasar ciki harda dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

Hotuna Da Bidiyon ‘Babur Day’ Na Auren Diyar Tukur Buratai, Amarya Fatima Ta Hadu Matuka

A yanzu kuma an gudanar da liyafar kunshin amarya inda Fatima da kawayenta suka fito shar da su gwanin ban sha’awa.

Fatima da kawayenta
Hotuna Da Bidiyo Sun Bayyana Daga ‘Kunshin’ Fatima Shettima Hoto: fashionseriesng
Asali: Instagram

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Shafin fashionseriesng a Instagram ya fitar da wasu hadaddun hotuna da bidiyoyi na Amarya Fatima da zuka-zukan kawayenta cikin ado da kwalliya na kece raini.

Fatima ta yi shiga na doguwar riga irin na kasaitattun amare kanta dauke da lullubi yayin da yan matan amare suka kewayeta cikin shigarsu ta anko iri daya.

Hotuna Da Bidiyon ‘Babur Day’ Na Auren Diyar Tukur Buratai, Amarya Fatima Ta Hadu Matuka

A gefe guda, mun kawo cewa ana ta shagulgulan biki na yaran manya a Najeriya tun a cikin makon jiya, kuma a wannan karon ma za a sake komawa jihar Borno ne.

A makon jiya ne aka daura auren dan tsohon shugaban kasa Umaru Musa Yar’adua mai suna Shehu wanda ya lula jihar ta Borno wajen zakulo zukekiyar matarsa Yacine Sheriff.

Kara karanta wannan

Bidiyon Kayan Sa Lalle Na "Allah Amin" Da Dangin Ango Suka Kai Gidansu Fatima Shettima

Hakazalika a wannan makon akwai daure-dauren aure biyu da za a yi a jihar ta yankin arewa maso gabashin kasar na diyar tsohon gwamnan Borno, Kashim Shettima da kuma diyar tsohon shugaban hafsan Soji, Tukur Buratai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel