Sanatocin Jam'iyyun Hamayya Sun Fice Daga Majalisa Bayan Kira a Tsige Buhari

Sanatocin Jam'iyyun Hamayya Sun Fice Daga Majalisa Bayan Kira a Tsige Buhari

  • Wata hatsaniya ta ɓalle a zauren majalisar dattawan Najeriya bayan fatali da bukatar tattauna wa kan tsige shugaba Buhari
  • Shugaban marasa rinjaye, Sanata Aduda, ya bukaci majalisar ta tattauna kan matsalar tsaro da kuma tsige Buhari
  • Sanata Ahmad Lawan ya yi fatali da bukatar nan take, lamarin da ya fusata Sanatoci suka fice daga zauren

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Sanatocin jam'iyyun hamayya sun fice daga zauren majalisar Dattawa biyo bayan kira a tsige shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari daga kujerarsa.

Channels TV ta ruwaito cewa hakan ya biyo bayan wata Dirama da ta auku a zaman mambobin majalisar Dattaawa ta ƙasa yau Laraba a Abuja, babban birnin ƙasa.

Shugaban marasa rinjaye, Sanata Phillip Aduda, ya tada mahawara inda ya nemi shugaban majalisa, Sanata Ahmad Lawan, a tattauna kan yanayin tsaron ƙasar nan da kuma tsige shugaba Buhari.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Sanatoci sun yi barazanar tsige shugaba Buhari, sun ba shi wa'adin mako 6

Amma Sanata Lawan, wanda ke jagorantar zaman, ya yi fatali da buƙatar shugaban marasa rinjaye, inda ya bayyana cewa batun da ya ɗakko ya faɗi warwas a kan fuska.

Domin nuna fushi da abinda shugaban majalisa ya yi, Sanatocin jam'iyyun adawa da ba APC ba, suka miƙe tsaye, suka fice daga majalisar ana tsaka da zaman yau.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mun ba Buhari wa'adin mako shida - Aduda

Bayan abubuwan da suka faru, Sanata Aduda, ya yi jawabi ga manema labarai a bakin zauren majalisar a madadin fusatattun takwarorinsa.

A cewarsa, mambobin majalisar da ke ɓangaren adawa sun bai wa shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, mako Shida ya shawo kan matsalar tsaron da ta addabi Najeriya.

Bugu da ƙari, ya ce Sanatocin sun cimma matsayar cewa zasu fara bin matakan tsige shugaban ƙasa idan har ya gaza dawo da zaman lafiya a Najeriya cikin lokacin da suka ɗibar masa.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Jam'iyyar APC ta zaɓi sabon shugaba a majalisar Dattawan Najeriya

A wani labarin kuma Gwamnoni arewa uku da wasu jiga-jigan APC sun sa labule da Tinubu, Shettima a Abuja

Gwamna El-Rufai na jihar Kaduna da wasu gwamnonin arewa biyu sun ziyarci jagoran APC na ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a Abuja.

Abokin takarar Tinubu, Sanata Kashin Shettima, Sakataren APC na ƙasa da tsohon shugaba, Oshiomhole sun halarci taron.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262