Yanzu-Yanzu: Alkali ya tasa keyar fitaccen lauyan kare hakkin bil'adama zuwa magarkama
- A ranar Laraba, 27 ga watan Yuli ne aka yankewa wani lauya mazaunin Legas, Inibehe Effiong hukuncin zuwa gidan gyaran hali na Uyo
- Mai shari’a Ekaette Obot ne ya karanta hukuncin a yayin zaman da Effiong ke kare wanda yake karewa a karar da Gwamna Udom Emmanuel ya shigar
- An yi zargin cewa Effiong ya kalubalanci batun alkalin ne bayan ya ki amincewa da mai shari'a Obot a korar wani dan jarida da ya zo ya daukar rahoto a zauren kotun
Akwa Ibom – Babban alkalin kotu a jihar Akwa Ibom, Mai shari’a Ekaette Obot ya tasa keyar Inibehe Effiong wani lauyan kare hakkin bil’adama a jihar zuwa gidan yari.
A wani sako da ya wallafa, a ranar Laraba, 27 ga watan Yuli, Lauyan da ke zaune a Legas ya yi ikirarin cewa ya soki hukuncin da mai shari’a Obot ya yanke saboda “kare Leo Ekpenyong a karar da Gwamna Udom Emmanuel ya shigar a gaban kotu”, inji Premium Times.
A cewarsa:
"Babban alkalin jihar Akwa Ibom, Mai shari'a Ekaette Obot, ya keyata zuwa gidan yari na tsawon wata guda saboda kare Leo Ekpenyong a karar da Gwamna Udom Emmanuel ya shigar a gaban kotu."
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Da yake karin haske kan yadda kotun ta yanke hukuncin, Effiong ya ce alkalin kotun ya kori wani dan jarida ne daga zauren kotun inda ya yanke hukunci a lokacin da ya ki amincewa da matakin tare da bayyana cewa ana sa ran za a saurari karar.
Ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa:
“Babban alkalin Akwa Akwa Ibom ya umarci wakilin Premium Times da ya bar kotun. Na ce ya mai shari'a, muna tunanin tun da abin na jama’a ne, a bar jama’a su lura da yadda abin ke gudana. Mai shari'a ya tambaye ni in ci gaba da yin tambayoyi na.
“Zan tafi Cibiyar Gyaran Hali ta Uyo a yanzu haka. Ban yi komai ba. Ban ma sami damar cewa komai ba kafin yanke hukuncin. Lauyoyi biyu a kotu sun nemi sassauci daga mai girma mai shari'a amma ya dage cewa dole ne a daure ni.”
Da ya isa gidan gyaran halin, an ki amincewa da Effiong ya shiga saboda ka'idar Korona, kuma za a tsare shi a gidan yarin Ikot Ekpene.
Ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa:
"Sun ce ba zai yiwuwa a daure ni a gidan yari na Uyo ba saboda ka'idar Korona dole ne in zauna a gidan yarin Ikot Ekpene. An ki karba ta kurkukun Uyo.
"Yanzu za mu koma kotu domin mai shari'a ya tantance inda ya kamata a daure ni, tarihi zai tabbatar da adalci."
Kawai ka bude gidajen yari kowa ya fito: Babban Lauya ga Buhari kan yafewa Nyame da Dariye
A wani labarin, Shararren Lauya, Femi Falana, a ranar Juma'a, ya yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya bude gidajen yari gaba daya a saki dukkan wadana aka daure kan laifin sata.
Falana ya bayyana hakan ne yayin jawabi a taron tunawa da marigayi Yinka Odumakin a jihar Legas, rahoton Vanguard.
Ya bayyana cewa kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadi adalci da daidaito tsakanin yan kasa saboda haka wajibi ne a saki dukkan wadanda tsare a kurkuku kan laifin sata.
Asali: Legit.ng