Kawai ka bude gidajen yari kowa ya fito: Babban Lauya ga Buhari kan yafewa Nyame da Dariye

Kawai ka bude gidajen yari kowa ya fito: Babban Lauya ga Buhari kan yafewa Nyame da Dariye

  • Femi Falana ya ce tun da Buhari ya yafewa abokansa da suka sace biliyoyin naira, toh wajibi ne ya saki sauran kananan barayi
  • Shahrarren lauyan yace idan bai sake su sai ya shawarci lauyoyinsu su kai kara kotu saboda wannan rashin adalci ne
  • Shugaba Buhari a jiya ya yi afuwa ga tsaffin gwamnoni biyu da aka jefa kurkuku kan satar dukiyar al'umma

Legas - Shararren Lauya, Femi Falana, a ranar Juma'a, ya yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya bude gidajen yari gaba daya a saki dukkan wadana aka daure kan laifin sata.

Falana ya bayyana hakan ne yayin jawabi a taron tunawa da marigayi Yinka Odumakin a jihar Legas, rahoton Vanguard.

Ya bayyana cewa kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadi adalci da daidaito tsakanin yan kasa saboda haka wajibi ne a saki dukkan wadanda tsare a kurkuku kan laifin sata.

Kara karanta wannan

Ko Buhari ya sauka matsalar tsaro ba za ta kare ba, Fadar Buhari ga dattawan Arewa

Yace:

"Najeriya ta zama abin dariya........Suna yafewa kawunansu, mutumin da yace ya zo yaki da rashawa yanzu shi ke yafewa mutumin da ya wawaure biliyoyin naira."
"Tsokaci na shine kawai a saki dukkan yan ta'adda, barayi dake gidajen yari."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Karkashin sashe na 17, ance ayi daidaito tsakanin yan kasa kuma sashe na 42 ya ce kada a nuna banbancin bisa arzikin mutum, kabilarsa ko wani abu, saboda haka ba zaka tsame mutum biyu ka bar sauran a wajen ba."
"Idan gwamnati bata saki sauran ba, zan baiwa lauyoyin sauran dake kurkuku su shigar d akara kotu bisa banbancin da aka nuna."
"Idan za ka yafewa abokanka, wajibi ne dukkan sauran barayin su samu."

Femi Falana
Kawai ka bude gidajen yari kowa ya fito: Babban Lauya ga Buhari kan yafewa Nyame da Dariye
Asali: UGC

Buhari ya yafewa Joshua Dariye, Jolly Nyame, da wasu fursunoni 157

Majalisar kolin kasa (masu mulki da tsaffin shugabanni) ta yafewa tsohon gwamnan jihar Taraba, Jolly Nyame da tsohon gwamnan Plateau, Joshua Dariye, dake garkame a kurkuku yanzu.

Kara karanta wannan

Yan bindiga da yan Boko Haram sun fara alaka da juna, Gwamnatin tarayya ta sanar

Gwamnonin biyu na cikin fursunoni 159 da majalisar ta yafewa ranar Alhamis karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari ranar Alhamis a birnin tarayya Abuja.

Daga cikin wadanda aka yafewa tsohon soja da minista lokacin Abacha, Tajudeen Olanrewaju; Laftanan Kanar Akiyode, da dukkan Sojojin da aka daure kan laifi a hannu cikin yunkurin juyin mulkin Gideon Orkar a 1990.

A cewar wata majiya daga fadar shugaban kasa, an yafewa tsaffin gwamnonin biyu ne bisa lafiya da yawan shekarunsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel