Yadda Jama’a ke yi wa Buhari Kaca-kaca a kan taya Tobi Amusan murnar cin tsere

Yadda Jama’a ke yi wa Buhari Kaca-kaca a kan taya Tobi Amusan murnar cin tsere

  • A makon nan aka tashi da labarin farin cikin nasarar da Tobi Amusan ta samu a gasar tseren Duniya
  • Amusan wanda ‘Yar Najeriya ce ta samu gwal, ta kafa tarihi a wasannin Athletics Championships 2022
  • A lokacin da ake wannan farin ciki, matsalar tsaro na cigaba da ta’azzara a yankin Arewacin Najeriya

Abuja - Muhammadu Buhari ya fito shafinsa na Facebook, yana mai taya Tobi Amusan murnar zama zakara da tayi wajen gasar tseren Duniyan.

Legit.ng Hausa ta fahimci mutane suna ta sukar Mai girma Muhammadu Buhari, suna zarginsa da rashin maida hankali kan halin da jama'a ke ciki.

A nan mun tattaro abin da wasu daga cikin masu magana a shafin shugaban na Najeriya ke fada:

Kara karanta wannan

Daga kwanciya bacci, Ɗan shugabar Kotun ɗaukaka ƙara ta Najeriya ya rasu

Ita Hauwa'u Aminu Korau, salati ta rika rangadawa, haka zalika wani Amb. Funtua da ya rubuta:

Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un
Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un
Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un
Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un
Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un
Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un
Allah ya isa tsakanin mu dakai baba

Shi kuwa YM Yusuf, sai ya kawo Hadisin Manzon Allah SAW, yana cewa akwai ranar amsa tambayoyi a lahira.

Allah Ya Isa.

- Bilal Muhammad Bello

Zamanka shugaban kasa yana cikin mafi munin masifar da aka taba samu a kasar nan. Allah ya sa ka da mu yi kewanka a 2023. Amin.

- Abdulkarim Umar

Ka gaza ko ta ina

- Ayman Ado

Allah ya shirya

- Ibrahim Mohammed

Shugaban kasa
Shugaba Muhammadu Buhari da Tobi Amusan Hoto: Muhammadu Buhari/BBC
Asali: Facebook

Buhari zai je Laberiya

Ana haka sai ga labarin cewa Muhammadu Buhari zai ziyarci kasar Laberiya domin taya su bikin murnar cika shekara 175 da samun ‘yancin kai a bana.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi garkuwa da wani Babban Malami a mahaifar gwamnan jihar Sokoto

A nan ma mutane sun yi ta sukar shugaban na Najeriya musamman a shafin BBC Hausa. Ga kadan daga abin da mutanen Facebook suke fada tun jiya:

Lamarin Buhari fa Wallahi akwai abin tsoro a ciki.

- Sa’ad Masama

Babu abin da zan iya fada maka sai dai Allah ya isa kawai!

- Yazid Alhassan

Kaico! Muna Allah wadai da salon shugabancinka Buhari

- Bashir Arma Ibrahim

Shi kuma wani mutumi cewa kurum ya yi: “Akwai Allah fa!”

Zaka dawo cikin 'yan uwan ka talakawa zamuga dawane ido zaka kallemu.

- Adamu Ciroma Mohammed

Ba ka kyauta mana ba.

- Haydar Aliyu Lawal

Yakubu Musa yana ganin ba laifin shugaban kasar ba ne;

Allah Sarki Baba Manjo, sai yadda su ka ga daman turaka. Allah ya kyauta

Shi kuwa wannan ya dauko abin da zafi, ya rubuta:

“Allah ya tsinewa wanan tafiya albarka.”
“Allah wadaran naka ya lalace,ka kasa gyara ƙasarka, sai gantali da yawon ta zubar a kan iska.”

Kara karanta wannan

2023: Sanusi II ya yi Jawabi a Game da Zabe, ya Bayyana cikas 1 da ake Fuskanta

- Aminu El – Shuaib

Abubakar Sadiq Kabir yake cewa: “Mutumin da bai fita ruwa ba amma wai shi yake kokarin matse wando!. Mtswww!’”

Laberiya fa?, IKON ALLAH

- Abdallah Amdaz

Ayi wa shugabanni addu'a ba zagi ba

Wani Ali Nuhu ya bada shawarar a daina sukar shugabanni, ya ce “Allah muke roko Ya shiryar da shugabanninmu Amin.

Raslan Mustafa ya yi wuf, ya maida masa martani da cewa:

“Ku dai kun taka rawa wajen tallata azzalumar wannan gwamnatin domin kyautata zato akanta, yanzu ta gaza angano inda ta nufa yakamata kuyi abunda yadace agabar da ta dace domin kiyaye hakkin yardar da mabiyanku sukai muku.”

Lauya ya kai APC da Tinubu kotu

Dazu an ji labari wani Lauya, Osigwe Momoh yana kalubalantar tikitin Musulmi da Musulmi a kotu, yana iya kawowa takarar APC a zaben 2023 barazana.

Barista Osigwe Momoh yace dokar kasa ba ta halastawa Bola Tinubu dauko wani Musulmi ya zama abokin takararsa ba, ya roki a hana APC shiga takara.

Kara karanta wannan

Na kadu: An kashe dan uwan shugaban PDP, Buhari ya sha alwashin daukar mataki, ya kakkausan martani

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng