Da duminsa: Shugaba Buhari zai shilla Liberia don taya su murnar shekaru 175 da samun 'yanci

Da duminsa: Shugaba Buhari zai shilla Liberia don taya su murnar shekaru 175 da samun 'yanci

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai dira kasar Liberia domin taya su murnar cika shekaru 175 da samun 'yancin kai.
  • Ana sa ran zai bar babban birnin tarayya Abuja a ranar Talata inda zai isa birnin Monrovia duk da ranar Talatan
  • Zai samu rakiyar ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama da darakta jana na NIA, Ambasada Ahmed Rufai

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai garzaya kasar Liberia inda zai sauka a birnin Monrovia a ranar Talata domin halartar shagalin bikin murnar cike shekaru 175 da samun 'yancin kan kasar.

Shugaban kasan kamar yadda Malam Garba Shehu ya sanar a ranar Litinin, zai bar babban birnin tarayya a ranar Talata.

Buhari zai yi tafiya
Da duminsa: Shugaba Buhari zai shilla Liberia don taya su murnar shekaru 175 da samun 'yanci. Hoto daga Garba Shehu
Asali: Facebook

Zai zama bako na musamman a wurin taron kuma zai shiga cikin sauran shugabannin kasashen duniya da kungiyoyi domin taya jama'ar Liberia murna a taron mai taken: "Tabbatar da hadin kai, kare zaman lafiyanmu domin cigaba da yalwar arziki."

Kara karanta wannan

Fitaccen malami: APC faduwa za ta yi a zaben 2023 mai zuwa saboda duk musulmai ne 'yan takarar

Shugaban kasan zai samu rakiyar tawagarsa da ta hada da ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama da darakta jana na NIA, Ambasada Ahmed Rufai Abubakar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ana sa ran dawowarsa gida Najeriya a ranar Talatan bayan sun kammala abinda ya kai su.

Najeriya ta taka rawar gani wurin saisaita kasar Afrika ta yamman a farkon shekaru 1990 wanda hakan ya kai ga samar da mulkin damokaradiyya kuma ta cigaba da tallafawa kasar a fannoni daban-daban.

Shugaba Buhari Ya Naɗa Sabon Shugaban Hukumar FRSC Na Riƙo

A wani labari na daban, Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya amince da naɗin Mista Dauda Biu, a matsayin muƙaddashin shugaban hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa FRSC biyo bayan ritayar Boboye Oyeyemi.

Mista Oyeyemi ne ya sanar da haka yayin miƙa al'amuran jami'an hukumar ga Biu a hedkwatar FRSC da ke birnin tarayya Abuja ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa ya Bada Sabon Mukami, ya Maye Gurbin Wanda ya ba Minista a Kano

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da kakakin hukumar FRSC, ACM Bisi Kazeem, ya fitar yau Litinin a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel