Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Ganduje ta hana ayyukan yan Adaidaita sahu bayan karfe 10:00 na dare

Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Ganduje ta hana ayyukan yan Adaidaita sahu bayan karfe 10:00 na dare

  • Gwamnatin Kano ta sanar da dokar hana ayyukan Keke Napep bayan ƙarfe 10:00 na dare kuma zata fara aiki ranar Alhamis
  • Hakan ya biyo bayan yawaitar amfani da yan Adidaita sahu wajen aikata muggan laifuka a jihar, a cewar kwamishinan labarai
  • Ibrahim Garba ya ce an yi haka ne domin kare rayuka da dukiyoyin al-umma, yan Adaidaita zasu yi aiki daga 6:00 na safe zuwa 10:00 na dare

Kano - Gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagoncin gwamna Abdullahi Ganduje ta hana 'yan Adaidaita sahu aiki bayan ƙarfe 10:00 na dare, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Sabuwar dokar na ƙunshe ne a wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano, Malam Muhammad Garba ya fitar ranar Litinin, ya ce dokar zata fara aiki ne ranar Alhamis 21 ga watan Yuli, 2022.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Jami'an tsaro sun buɗe wa baƙin ɗaura aure wuta, sun kashe da dama

Adaidaita sahu.
Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Ganduje ta hana ayyukan yan Adaidaita sahu bayan karfe 10:00 na dare Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Kwamishinan ya kara da bayyana cewa gwamnati ta cimma matsaya kan sanya dokar ne a ƙarshen taron tsaro na jihar Kano.

"Mun ɗauki wannan matakin ne a wani ɓangaren kokarin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al'umma a dukkan sassan jihar Kano," a cewar Kwamishinan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malam Garba ya roki masu Adaidaita sahu su bi dokar sau da ƙafa, inda ya ƙara da cewa jami'an tsaro za su bi kurfa-kurfa don tabbatar da ana bin dokar ba tare da jayayya ba.

A ruwayar jaridar Daily Trust, bayan sanya wannan dokar hanin, masu Adaidaita sahu za su rika aikin su daga ƙarfe 6:00 na safe zuwa ƙarfe 10:00 na dare a kowace rana.

Meyasa gwamnatin Kano ta ɗauki wannan matakin?

Bayanai sun tabbatar da cewa an samu jerin aikata manyan laifuka a jihar Kano, wanda zaka ga ko dai yana da alaƙa da yan Adaidaita ko kuma da taimakon su, wanda sakamakon haka an rasa rayuka da muhimman abubuwa.

Kara karanta wannan

Jerin gwamnonin da suka sha ƙasa a zaɓe yayin da suka yi yunƙurin tazarce kan kujerun su a Najeriya

Legit.ng Hausa ta zanta da wasu mazauna Kano kan yadda suka ji da wannan sabuwar dokar, wasu sun nuna jin daɗin su duba da abubuwan da ke faruwa wasu na ganin za'amatsa wa wasu.

Sunusi Isiyaku, wani mazaunin Anguwar Hotoro kusa da NNPC Depot ya shaida wakilin mu cewa abin da mai girma gwamna ya yi dai-dai ne, duba da sace-sace da ke kai wa da jikkata mutane ta hanyar amfani da Adaidaita sahu.

Sanusi ya kuma yi kira da gwamnati ta tabbata mutane sun bi dokar sau da ƙafa, amma ya buƙaci a rangwanta wa waɗan da ka iya yuwuwa lalura ce ta rashin lafiya ta fito da su.

Sai dai a nashi hangen, Bashir Zakiru, ya ce babu wanda zai soki dokar duba da an yi ta ne domin al'umma amma a cewarsa masu sana'a irin tasa da ke kai wa dare zasu shiga matsala.

Ya ce ya kan kai ƙarfe 1:00 na dare kafin ya rufe shagon sana'arsa kuma Adaidaita sahu ce hanya mafi sauki ta zuwa gida a irin wannan lokacin.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shahararriyar jarumar Fim a Najeriya ta yanke jiki ta faɗi, ta rasu tun kafin zuwa Asibiti

Wani Bakano da ya nemi a sakaya sunansa ya ce tabbas ana amfani da Adidaita Sahu ana kwace da sauran ayyukan laifi da daddare, amma ya masu sana'a nesa da gida zasu yi kenan.

A tunaninsa, wannan dokar ba zata hana cigaba da aikata irin wannan ɗanyen aikin ba, kuma tabbas masu sana'a da ke wuce irin wannan lokacin zasu shiga matsala.

A wani labarin kuma duk a arewa maso yamma, Hadimin gwamna Tambuwal da dandazon mambobi sun sauya sheƙa daga PDP zuwa jam'iyyar APC

Mai ba gwamna Aminu Waziri Tambuwal na Sokoto shawara ta musamman ya ja masoyansa sun sauya sheka daga PDP zuwa APC.

Honorabul Ibrahim Gidado, tsohon mamba a majalisar dokokin jihar, ya samu kyakkyawar tarba daga jiga-jigan APC.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel