Kin fi karfi na: Miji ya fece ya bar matarsa saboda ta haifa masa tagwaye sau biyar

Kin fi karfi na: Miji ya fece ya bar matarsa saboda ta haifa masa tagwaye sau biyar

  • Nalongo Gloria ta ba da labarinta mai ban tausayi da radadi na yadda mijinta ya fece ya bar ta da 'ya'ya ratata
  • Matar 'yar kasar Uganda ta ce mai gidanta Ssalongo ya watsar da kashinta bayan da ta haifi tagwaye har sau biyar
  • Mijin Gloria dai cewa yayi sam bai yarda hakan lafiya bane, don haka ba zai iya ci gaba da zama da ita, wannan yasa ya fece abinsa

Uganda - Tarin 'ya'ya dai albarka ce kuma abu mai kyau, amma sa'ad da aka samu tasgaro, zai iya haifar da hargitsi.

Wata mata da ta haifi tagwaye har sau biyar ta ba da labarinta mai radadin gaske na yadda tarin albarkar 'ya'ya ya zame mata nauyi.

Matar da ta haifi 'ya'ya rututu ta shiga tasku, mijinta ya tsere ya bar ta da 'ya'ya
Bani iyawa: Yadda magidanci ya fece ya bar matarsa saboda haifa masa tagwaye sau biyar | Hoto: NTV Mwasuze Mutya
Asali: Facebook

Ya kore ta daga gidansa

Nalongo Gloria daga Uganda ta ce mijinta Ssalongo ya watsar da kashinta ne saboda ta ci gaba da haifa masa tagwaye.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Gloria ta shaida wa NTV Mwasuze Mutya yayin wata hira da ta yi da cewa:

“Lokacin da na samu cikin tagwaye a rana ta uku, sai mutumin ya ce wannan ya fi karfinsa, ya ce in koma gida.
"A inda ya tura ni ba ni da lambarsu kuma saboda na zo Kampala ne aiki a matsayin boyi-boyi"

Wannan dai wani mafarin kunci ne ga Gloria, wadda da kyar ta sami wani wuri don neman taimako.

Ba zai iya zama da ita ba

Yayin da take makale cikin taskun wahala, mijin Gloria, Ssalongo, ya ba ta sharudda da ka'idoji, kamar yadda kafar labarai ta Tuko ta tattaro.

A cewarta:

"Mutumin ya gaya mani cewa idan ba zan iya haihuwar dai dai ba, ba zai iya kula da ni da karnuka na ba."

Wata rana, sa’ad da Gloria ke neman abin yi, sai ta gano cewa mijin nata ya tattara kayansa ya fece ya barta kurum.

Bata san inda yake ba, haka kuma ya bar ta cikin tashin hankalin raino da kula da tarin 'ya'ya.

Ta rasa yara har uku

A dai cikin irin wannan yanayi, Gloria ta rasa wasu ’ya’yanta, kamar yadda ta bayyana a cikin tattaunawar da aka yi da ita.

A cewarta:

"Da yanzu ina da ya'ya 10, amma biyu sun gudu, guda kuma ya mutu. Ina da bakwai. Wani mutum ne ya binne yaron a Zirobwe. Bai kai shi Masaka ba."

Lokacin kullen Korona, Gloria ta gaza iya rike tarin 'ya'yanta ga kuma kudin haya.

Haka dai abubuwa suka ta dagule mata, hakan ya tilasta mata neman wani wurin da za ta tsira da ‘ya’yanta.

Ba ta nadamar haifar 'ya'ya rututu

Duk da kalubalen da take fuskanta, Gloria ba ta nadamar samun irin wannan babban dangi mai 'ya'ya rututu, tare da bayyana cewa Allah ne mai iko ya bata su.

A cewarta:

“Bana nadamar haihuwar yaran nan duka, na san mahaifinsu baya son su, kuma ba zan iya ajiye su a wurinsa ba, duk da kalubalen da nake fuskanta, ba zan taba watsi da ‘ya’yana ba, na san Allah zai azurta su. .
"Na mika lamurra na ga Ubangiji, a yanzu haka mai gidan da nake zaune a ciki ya ce min ba ya so na da kayana barkatai ga kuma 'ya'ya rututu irin wannan, na sha wahala amma Allah ne mafi sanin abin dake gaba."

Zargin cin amana: Hotunan magidanci da ya sheke matarsa, ya mika kansa hannun 'yan sanda da muhimmiyar shaida

A wnai labarin na daban, magidanci mai shekaru 55 ya sheke matarsa mai shekaru 45 bayan ya zargeta da cin amanarsa kuma daga bisani yayi tafiyar kusan kilomita 12 zuwa ofishin 'yan sanda da kanta.

Lamarin ya faru ne a Chandrasekharpur dake yankin Odisha Dhenkanal a sa'o'in farko na ranar Juma'a, 15 ga watan Yulin 2022.

Bidiyon mai matukar ban tsoro na mutumin yana tafe da kan matarsa da ya sheke ya yadu a kafafen sada zumuntar zamani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel