An gudanar sa Sallar jana'izar jarumin soja, Manjo MM Hassan
An gudanar da jana'izar kwamanda soji, Marigayi Manjo MM Hassan (Sarkin Yakin Damboa) a garin Maimalari, Maiduguri.
Dandazon jama'a sun halarci Sallar jana'izar babban kwamandan rundunar Operation Lafiya dole, Manjo MM Hassan, wanda aka gudanar a yau Asabar, 13 ga watan Janairu, 2017 a garin Maimalari, garin Maiduguri a jihar Borno.
Marigayin ya rasa rayuwarsa ne a filin daga yayinda suke artabu da yan tada kayar bayan Boko Haram.
KU KARANTA: Yadda wata 'yar shekaru 14 ta taimakawa 'yar Chibok wajen kubuta daga Boko Haram
An siffanta rasuwan Manjo Hassan a matsayin babban rashi ga hukumar soja saboda irin jaruntan da marigayi ke nunawa wajen yakan yan ta'adda a yankin Arewa maso gabashin Najeriya.
Manyan sojoji da yan siyasa sun halarci wannan jana'iza. Daga cikin sune babban hafsan sojin Najeriya, Laftanan Janar Tukur Buratai; gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima da sauran su.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng