Budurwa ta kai saurayi kotu kan ya ki zuwa wurin shakawatar da suka yi za su hadu, tana bukatar diyyar N4m

Budurwa ta kai saurayi kotu kan ya ki zuwa wurin shakawatar da suka yi za su hadu, tana bukatar diyyar N4m

  • Wata budurwa 'yar asalin Michigan mai suna QaShontae Short, bata sassauta ba bayan wani saurayinta ya ki zuwa inda suka yi zasu hadu
  • An gano yadde ta maka Richard Jordan a gaban kotu inda take bukatar diyyar N4 miliyan sakamakon damuwar da ya saka ta ciki
  • A wani bidiyon zaman kotu da ya bayyana a kafafen sada zumunta, an ga Short na sa'insa da alkalin kotun

Wata budurwa ta fusata sakamaakon yadda matashi ya yi watsi da ita bayan yayi alkawarin fita da ita. Ta sake fusata inda fushin ya bayyana kan yadda ta yanke shawarar maka shi a kotu tare da bukatar diyyar N4 miliyan, Daily Mail ta ruwaito.

Sues Boyfriend
Budurwa ta kai saurayi kotu kan ya ki zuwa wurin shakawatar da suka yi za su hadu, tana bukatar diyyar N4m. Hoto daga Daily Mail/Facebook
Asali: UGC

Kamar hakan bai isa ba, bidiyon da tuni ya yadu ya bayyana matar mai suna QaShontae Short yayin da ta fusata da alkalin yayin zaman kotun da ake yi ta yanar gizo wanda ya tada tarzoma.

Kara karanta wannan

Satar kudin al'umma: Kotu ta ce a ci gaba da rike Akanta Janar a magarkama

Kama yadda New York Post ta wallafa, Short ta maka karar ne a 2020 inda take zargin Richarda da kin bayyana kuma ya bar ta a rana bikin zagyowa haihuwa mahaifiyarta wacce ta rasu daga bisani, kamar yadda takardun shari'ar da TMZ suka samu suka nuna.

Mata mai karfin hali ta maka Jordan a kotu kan yadda da gangan ya hana ta nastuwa tare da sanya ta cikin kunar rai.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ana rahoto cewa, an yi shar'ar ne ta yanar gizo ya koma hargitsi inda Short ta samu rashin jituwa da alkalin kan ko cewar ko rashin bayyana Jordan laifi ne a shari'ance.

Alkali Herman Marable Jr, wanda zai yanke hukunci kan shari'ar yace bashi da hurumin hukuncin wannan shari'ar a kotun yanki inda yace ta kai ta kotun da ta dace.

Budurwa ta kai karar magidanci wurin matarsa bayan yayi mata karyar mutuwar matarsa

Kara karanta wannan

Budurwa ta kai karar magidanci wurin matarsa bayan yayi mata karyar mutuwar matarsa

A wani labari na daban, Dani Bose, kyakyawar Baturiya ta fallasa wani mutum da suka kwashe shekaru 30 da matarsa da aure amma yake neman matan banza a waje.

Budurwa mai shekaru 21 kuma tauraruwa TikTok ta bayyana yadda magidancin yayi ikirarin cewa matarsa ta mutu kuma yake son su hadu domin lalata.

A bidiyon, ta bayyana yadda matarsa ta neme ta kuma tace tana son ta gwada mata cewa ko mijinta da suka yi shekaru 30 suna tare yana cin amanarta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel