Jerin ibada 8 da ake bukatar duk Musulmi ya dukafa da aikatawa a farkon Dhul Hajj

Jerin ibada 8 da ake bukatar duk Musulmi ya dukafa da aikatawa a farkon Dhul Hajj

  • A halin yanzu an shiga watan Dhul Hajjin 1443, wanda yana cikin watanni mafi daraja a Musulunci
  • Malaman addini sun yi magana game da ibadun da suka dace duk wani Musulmai ya dukufa a kan su
  • A cikin wannan wata na Dhul Hajj ne Musulmai daga fadin Duniya suke iya gudanar da aikin Hajji

Kaduna - A wani rubutu da Farfesa Ahmed Bello Dogarawa ya yi, ya yi bayani game da wannan wata mai alfarma da irin ibadun da ake so a rika yi a cikinsa.

Farfesa Ahmed Dogarawa wanda malami ne a jami’ar ABU Zaria ya yi rubutun ne tun a 2020. A wannan karo, Legit.ng ta dawo da ita saboda muhummancinta.

Wannan malami wanda ya kware a ilmin addini da na zamani, ya nakalto jawabin manyan malamai irinsu Ibn Rajab Al-Hambali da su Ahmed Ibn Taimiyyah.

Kara karanta wannan

Hajjin bana: Lokaci yana nema ya kure, har yanzu ba a dauki 50% na Maniyyatan Najeriya ba

A rubutun na shi, ya ambaci darajar yin azumi a cikin kwanaki takwas na farkon watan Zul-Hijjah, musamman azumin ranar Arafah ga wadanda ba mahajjata ba.

Farfesan ya tabo maganganun malamai a kan darajar yawaita Kabbarbari da yin addu’o’i da zikiri a ranar Arafa, wanda ita ce za ta kasance rana ta tara a Dhul Hajj.

Daga cikin ibadun da suka kebanta da watan akwai layya, watau yanka dabba daga rana ta goma.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Musulmi a Dhul Hajj
Masu Hajji a ranar Arafah Hoto: www.hiiraan.com
Asali: UGC

1. Azumin Arfa

Hadisai ingantattu sun tabbatar da falalar yin azumi a ranar Arfa, wato, ranar tara ga watan Zul-Hijjah, ga wanda ba ya cikin ayyukan Hajji. Muslim ya ruwaito Hadisi daga Abu Qatādah (Allah Ya yarda da shi), Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi) ya ce: “Azumin Arfa, ina fatan ya kankare (zunuban) shekarar da ta gabata da wacce za ta zo.” A ruwayar Ibn Mājah daga Qatādah dan Nu’umān (Allah Ya yarda da shi), Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi) ya ce: “Wanda ya azumci ranar Arfa, za a gafarta masa (zunuban) shekarar da ta wuce da wacce za ta zo.”

Kara karanta wannan

Tallafin fetur: Majalisa za ta binciki Gwamnatin Buhari, ta ce an sace Naira Tiriliyan 2.9

2. Azumi

Hadisin da Abdullahi dan Abbās (Allah Ya yarda da su) ya ruwaito game da falalar kwanaki goma na farkon watan Zul-Hijjah ya tabbatar da cewa kyawawan ayyuka sun fi soyuwa ga Allah a cikin wadannan ranaku. Babu shakka, azumi yana daya daga cikin mafi alherin kyawawan ayyuka da za a iya yi don neman lada da samun kusanci zuwa ga Allah (Mai girma da daukaka) a cikin wadannan kwanaki. Bisa la’akari da wannan Hadisi, za a iya yin azumi a farkon watan Zul-Hijjah, tun daga ranar daya ga wata har zuwa takwas ga wata, daga nan kuma a yi azumin Arfa a ranar tara ga wata.Banda ma Hadisin Abdullahi dan Abbās (Allah Ya yarda da su), kwadaitarwa game da yin azumi cikin kwanaki takwas na farkon watan Zul-Hijjah ta zo karara cikin wani Hadisi. Abu Dāwud da Nasā’ī sun ruwaito daga Hunaydah dan Khālid daga matarsa cewa wadansu daga cikin matan Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi) sun ce: “Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi) ya kasance yana azumi cikin kwanaki tara na (farkon watan) Zul-Hijjah, da ranar ‘Āshūrā, da kwanaki uku a cikin kowane wata, da kuma ranakun litinin da alhamis na kowane wata.” Sheikh Albānī ya bayyana ingancin hanyar da aka ruwaici Hadisin a cikin Sahīh Sunan Abī Dāwud.Duk da cewa akwai Hadisi wanda Muslim ya ruwaito daga Nana Ā’isha (Allah Ya yarda da ita) ta ce: “ban taba ganin Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi) ya yi azumi a goman farko na watan Zul-Hijjah ba”, Imām An-Nawawi a cikin littafin Al-Majmū’, da Ibn Rajab a cikin Latā’iful Ma’ārif, da Ibn Hajar a cikin Fathul Bārī, da Ash-Shaukānī a cikin Naylul Awtār, da wasu Malamai da yawa sun rinjayar da mustahabbancin yin azumi a cikin kwanaki takwas na farkon watan Zul-Hijjah, ko dai saboda Hadisin Abdullahi dan Abbās (Allah Ya yarda da su) ko kuma saboda la’akari da ka’idar gabatar da Hadisin da ya tabbatar da hukunci akan wanda ya kore hukuncin. Haka kuma, ruwayoyi da aka samu daga wasu Sahabbai da Tābi’ai cewa suna yin azumi a farkon watan Zul-Hijjah na daga dalilai da suke karfafa Hadisin Hunaydah dan Khālid. Misali, a cikin littafin Latā’iful Ma’ārif, Ibn Rajab ya bayyana cewa Abdullahi dan Umar (Allah Ya yarda da su) ya kasance yana yin azumi a cikin goman farko na Zul-Hijjah.Ba dole ne a azumci dukkan ranakun ba. Gwargwadon abinda mutum zai iya, shi ne zai yi. Haka kuma ba azumi ne kadai za a iya yi ba a wadannan ranaku. An fi son a yi nau’o’in ibada mabanbanta. Amma dai azumi na daga cikin mafi girman nau’o’in ibada da za a raya kwanakin da su.

Kara karanta wannan

Garkuwa da mutane: Alkali ya yanke hukunci a kan Budurwar da tayi karyar an sace ta

3. Kabarbari

Yana daga Sunnah, yawaita yin Takbīr (Allahu Akbar) da Tahmīd (Alhamdu Lil Lah) da Tahlīl (Lā ilāha illal Lah) da Tasbīh (Subhānal Lah) a cikin wadannan kwanaki guda goma. Tirmidhī ya ruwaito Hadisi wanda Sheikh Albānī ya tabbatar da sahihancinsa a cikin littafin Sahīh Al-Jāmi’ daga Abdullahi dan Umar (Allah Ya yarda da su) ya ce, Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi) ya ce:

مَا مِنْ أَيَّامٍ أَعْظَمُ عِنْدَ اللهِ، وَلاَ أَحَبُّ إِلَيْهِ مِنَ الْعَمَلِ فِيهِنَّ مِنْ هَذِهِ الأَيَّامِ الْعَشْرِ، فَأَكْثِرُوا فِيهِنَّ مِنَ التَّهْلِيلِ، وَالتَّكْبِيرِ، وَالتَّحْمِيدِ

“Babu wasu ranaku da suka fi girma a wajen Allah kuma ayyuka a cikinsu suka fi soyuwa wajen Allah kamar wadannan kwanaki goma (na farkon watan Zul-Hijjah). Don haka, ku yawaita Tahlīl (fadin Lā ilāha illal Lah) da Takbīr (fadin Allahu Akbar) da Tahmīd (fadin Alhamdu lil Lah) a cikinsu.”Ana yin wannan zikiri ne a bayyane. Kuma ana iya yinsa a kowane wuri, (kamar gida, kasuwa, kan titi, da sauransu) banda wuraren da aka samu nassi sahihi da ya hana a yi. Kabbarbarin na iya daukar sīgar: Allahu Akbar, Allahu Akbar, lā ilāha illal Lah, wal Lāhu Akbar, wa Lillāhil Hamd; ko kuma duk wata sīga mai kyawun ma’ana, musamman wadanda Sunnar Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi) ta tabbatar. Kabbarbari a wadannan ranaku, wata Sunnah ce da mafi yawancin mutane suka manta da ita. Da wahala mutum ya ji ana yin kabbarbari a wadannan ranaku, musamman daga farko-farkon watan. Ya kamata a raya wannan Sunnah ta hanyar yin wannan zikiri a bayyane kuma a duk inda aka samu dama. Bukhāri ya ruwaito, “Abdullahi dan Umar da Abu Hurairah (Allah Ya yarda da su) sun kasance suna yin wadannan kabbarbari a cikin kasuwa (don tunatar da mutane muhimmancin yin su) kuma sai mutane su ma su yi kabbarbarin.” Haka kuma Sayyiduna Umar (Allah Ya yarda da shi) ya kasance yana yin kabbarbari a cikin hemarsa, a Muna (lokacin aikin Hajji). Da yawa daga malamai sun ce kabbarbarin da ake yi a wannan lokaci sun kasu gida biyu: Mutlaq (wanda bai da iyakantaccen lokaci) da Muqayyad (wanda aka kebe wa lokaci). Kowanne daga cikinsu ya tabbata a sahihiyar Sunna ta Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi). Mutlaq shi ne wanda za a yi tun daga daya ga wata har zuwa goma ga wata. Muqayyad kuwa shi ne wanda za a yi daga bayan sallar asuba na ranar Arfa zuwa sallar la’asar na ranar sha uku ga wata. A cikin Fathul Bārī, Ibn Hajar ya bayyana cewa fara yin wadannan kabbarbari daga bayan fitowar alfijir na ranar Arfa shi ne bayani mafi inganci da aka ruwaito daga Sahabban Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi).

Kara karanta wannan

Cikakken jerin Sanatoci 58 da aka zazzage, ba za su koma kujerunsu a Majalisar Dattawa ba

4. Addu’o’i da ambaton Allah

Muslim ya ruwaito Hadisi daga Abdullahi dan Umar (Allah Ya yarda da su) ya ce, Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi) ya ce:

خَيْرُ الدُّعَاءِ دُعَاءُ يَوْمِ عَرَفَةَ، وَخَيْرُ مَا قُلْتُ أَنَا وَالنَّبِيُّونَ مِنْ قَبْلِي: لَا إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ وَحْدَهُ لَا شَرِيكَ لَهُ، لَهُ المُلْكُ وَلَهُ الحَمْدُ وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ

“Mafi alherin addu’a ita ce addu’ar (da aka yi) ranar Arfa, kuma mafi alherin abinda ni da Annabawa kafin ni muka fada (a ranar Arfa) shi ne: Lā ilāha illāl Lah Wahdahu lā sharīka Lah, Lahul Mulk wa Lahul Hamdwa Huwa alā kulli shay’in Qadīr.”

5. Aikin Hajji da Umrah

Hajji da Umrah na daga mafifitan nau’o’in ibada da ake yi a cikin watan Zul-Hijjah. Hadisi ya tabbata cewa Aljanna ce sakamakon aikin Hajji da ya kubuta daga sabon Allah da rashin bin ka’idodin Sharī’ah wajen gudanar da shi.

6. Ibadar Layya

Kara karanta wannan

Kuma dai: Yan bindiga sun sake sace wani limamin Katolika a jihar Edo

Ana yin layya ce ta hanyar yanka dabba daga cikin nau’o’in dabbobi guda uku (awaki da shanu da rakuma) daga ranar goma ga watan Zul-Hijjah (bayan an yi sallar idi) zuwa sha uku ga wata, don neman kusanci ga Allah (Mai girma da daukaka). Kasancewa ranar goma ga Zul-Hijjah ce rana ta farko ta yin layya, hakan ya nuna cewa layya tana cikin ayyukan da ake yi a goman farko na watan.Ibadar layya tana daga manya-manyan ibadodi a Musulunci. Tana kara tunatar da Musulmi kadaituwar Allah (Mai girma da daukaka), da falalar Allah akan al’umma, kuma tana tabbatar da tsantsar biyayyar babanmu Annabi Ibrahim (tsira da aminci su tabbata a gare shi) ga Allah (Mai girma da daukaka).

7. Sallar Īdi

Sallar īdi na daga cikin ayyukan alheri da ake yi cikin kwanaki goma na farkon watan Zul-Hijjah. Ana gudanar da ita a ranar goma ga wata, wato washegarin ranar Arfa. Ranar īidi na daga alamomi na Allah wadanda Musulmai a ko’ina cikin duniya ke yin bukukuwa da shagulgula don bayyana godiya ga Allah saboda samun nasarar kammala wata babbar ibada, da jaddada ‘yan uwantakar addini, da kuma taya juna murna da farin cikin zagayowar daya daga cikin ranakun da Musulunci ya ba muhimmanci. Īdul Adhā, wato īdin babban salla na biyo bayan nasarar kammala tsayuwar Arfa da mahajjata suka yi wacce ita ce rukunin aikin Hajji mafi girma.A wajen mafi yawan malamai, sallar īdi Sunnah ce mai karfi. Wadansu Malamai na ganin cewa mustahabbi ce, a yayin da wasu kuma suka tafi a kan wajabcinta. Salla ce da aka shar’anta ta ga Musulmi, maza da mata. Saboda muhimmancinta, Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) har umurni ya bayar game da fita don gabatar da ita, shi kuma a karan kansa, ya lazimce ta tun daga shekarar da aka fara yinta har zuwa lokacin da ya bar duniya. A cikin Hadisin da Bukhāri da Muslim suka ruwaito daga Ummu ‘Atiyyah (Allah Ya yarda da ita) ta ce: “An umurce mu da fitar da ‘yan mata (wadanda suka balaga) da matan aure da ke cikin dakunansu (har da wadanda ke cikin jinin al’ada) zuwa sallar īdi…” Haka kuma, Bukhāri da Muslim sun ruwaito Hadisi, Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya umurci macen da ba ta da mayafin da za ta sanya don halartar sallar īdi ta karbi aro wajen wacce ke da safayar mayafi (don dai kowa da kowa ya halarci sallar).

Kara karanta wannan

Zargin Cire Sassan Mutum: Jami'ar Lincoln A Birtaniya Ta Yi Hannun Riga Da Ekweremadu

8. Nau’o’in Ibada daban-daban

Ban da nau’o’in ibada da bayani ya gabata akansu, mutum yana iya yin duk wani aikin alheri da yake kusantar da bawa ga Allah (Mai girma da daukaka) don samun lada da kuma fatan dacewa da falalar wadannan kwanaki. Irin wadannan ayyuka sun hada da karatun Alkur’ani, da zikiri, da addu’a, da tuba daga zunubai, da yawaita istigfari, da salati ga Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi), da sadar da zumunta, da ziyara, da kyautata wa iyaye, da sadaka, da fitar da zakka (idan ta dace da lokacin).

Asali: Legit.ng

Online view pixel