Majalisar dattawa zata binciki Alkalin Alkalai da yayi murabus, Tanko Mohammad, bisa zargin rashawa

Majalisar dattawa zata binciki Alkalin Alkalai da yayi murabus, Tanko Mohammad, bisa zargin rashawa

  • Tsugunnu bata kare ba, majalisa ta bada umurnin a binciki tsohon Alkalin Alkalan Najeriya Tanko Mohammed
  • CJN Tanko ya yi murabus a jiya inda ya jingina hakan ga rashin lafiya da yake fama
  • Alkalan kotun koli guda 14 suna zargin Tanko Mohammed da babakere kan kudaden kula da sashen shari’a

Abuja - Majalisar dattawar Najeriya ta bayyana cewa zata gudanar da sabon bincike kan tsohon Alkalin Alkalan Najeriya, CJN Tanko Mohammad bisa zargin rashawa da sauran Alkalan kotun ke masa.

Kwamitin harkokin shari’a ta majalisar ta bayyana hakan a ranar Talata, 28 ga watan Yuni, 2022, rah rahoton Punch.

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Ibrahim Lawan, ya umurci kwamitin dake karkashin Sanata Opeyemi Bamidele, su binciki zargin da ake yiwa tsohon Alkalin.

Lawan yace:

“Majalisa na umurtan kwamitin shari’a ta cigaba da aikinta don nemo mafita daga rikicin dake faruwa biyo bayan kararrakin da Alkalan kotun koli suka shigar.”

Kara karanta wannan

An hana matar Ekweremadu ganinsa yayin da yaransu suka bayyana a kotu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tanko
Majalisar dattawa zata binciki Alkalin Alkalai da yayi murabus, Tanko Mohammad, bisa zargin rashawa
Asali: UGC

Jerin sunayen Alkalan kotun koli 14 da suka tuhumci Tanko da shan jar miya shi kadai

A farkon makon da ya gabata, alkalan kotun kolin Najeriya sun aikewa Alkalan Alkalai, Ibrahim Tanko Mohammed wasikar kar ta kwana bisa abubuwan dake gudana a babbar kotun Najeriya.

A wasikar da manema labarai suka gani, Alkalan kotun koli 14 sun tuhumci Alkali Tanko Mohammed da gazawa wajen gudanar da ayyukansa matsayin shugaba.

Abubuwan da Alkalan suka lissafa a wasikar sun hada da gidaje, motoci, lantarki, man Gas, yanar gizo a gidajen Alkalai, horo, da rashin wuta a kotuna.

Sun zargeshi da cin karansa ba babbaka yayinda yake hanasu kayan jin dadi.

Legit ta tattaro muku sunayen Alkalan kotun koli 14

Olukayode Ariwoola

Musa Dattijo Mohammed

Kudirat Motonmori O. Kekere-Ekun

John Inyang Okoro

Chima Centus Nweze

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Gwamnatin Neja ta ba da hutun kwanaki 2 don rajista da karbar PVC

Amina Adamu Augie

Uwani Musa Abba-Aji

Mohammed Lawal Garba

Helen Moronkeji Ogunwumiju

Abdu Aboki

Ibrahim Mohammed Musa Saulawa

Adamu Jauro

Tijjani Abubakar

Emmanuel Akomaye Agim.

Asali: Legit.ng

Online view pixel