Zamfara: Sabon Farmaki ya Tilasta Mazauna Mada da Wasu Kauyuka Barin Gidajensu

Zamfara: Sabon Farmaki ya Tilasta Mazauna Mada da Wasu Kauyuka Barin Gidajensu

  • Mazauna yankin Mada da wasu kauyuka karkashin karamar hukumar Gusau sun shiga cikin fargaba yayin da 'yan bindiga suka kai musu hare-hare daban-daban a jere
  • 'Yan bindiga sun kai hari Mada da kauyukan da ke makwabtaka tare da halaka 'dan sa kai 1 gami da garkuwa da mutane 7, sannan suka koma ranar Juma'a suka sake yin garkuwa da mutane 3
  • Hakan yasa mutanen yankin da dama suka tattara komatsansu tare da tserewa daga kauyukan, kafin gwamanatin jihar ta bada sanarwan yarjewa mutanen jihar mallakar bindigogi

Mada, Gusau - Mazauna yankin Mada da wasu kauyuka dake karkashin karamar hukumar Gusau sun tsere daga gidajensu bayan 'yan bindiga sun kai musu sabon farmaki.

Channels TV ta ruwaito cewa, Sabon harin 'yan bindigan da suka kai kwanan nan ya faru ne a ranar Alhamis, inda suka halaka wani 'dan sakai gami da garkuwa da kimanin mutane bakwai.

Kara karanta wannan

A Shirye Nake In Jagoranci Yaki da 'Yan Bindiga a Jihata, Gwamnan Bauchi

Unknown Gunmen
Zamfara: Sabon Farmaki ya Tilasta Mazauna Mada da Wasu Kauyuka Barin Gidajensu. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

A ranar Juma'a, 'yan bindigan sun sake kai wani harin a wani yankin Mada misalin karfe 5:00 na yamma, tare da bude wa mazauna yankin wuta gami da yin garkuwa da wasu uku.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Har ila yau a wannan ranar, 'yan bindiga sun kai farmaki anguwar Gidan Bangi na Ruwan-bore karkashin yankin Mada tare da halaka mutane 12.

Cigaba da kai hare-haren ne ya tilasta mazauna yankin da dama tserewa daga gidajensu tare da komawa yankunan da suka fi tsaro irinsu Kwatarkwashi.

Kamar yadda wani mazaunin yankin ya bayyana, mutanen yankunan da lamarin ya auku sun shirya yin zanga-zanga saboda irin farmakin da aka kai musu a jere, amma hukumomin tsaro suka dakatar da shirinsu.

Duk iya kokarin ganin an zanta da kakakin 'yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu bai yiwu ba, saboda bai dauki kiraye-kirayen wayar da aka yi masa ba.

Kara karanta wannan

Sokoto: 'Yan Bindiga Sun Halaka Manoma 11, Sun Kallafawa Wasu Harajin Noma

Sai dai, daga bisani gwamnatin jihar ta shawarci mutanen jihar da su mallaki bindigogi don kare kawunansu.

Sanarwar ta zo ne a wata takarda da kwamishinan jihar Zamfara, Ibrahim Dosara ya fitar a ranar Asabar.

"Daga yanzu gwamnati ta umarci mutane da su zama cikin shiri gami da mallakar bindigogi don kare kawunansu daga 'yan bindiga, kamar yadda gwamnati ta umarci kwamishinan 'yan sanda da ya bada lasisi ga duk wadanda suka cancanta kuma su ke da ra'ayin mallakar irin wandannan bindigogin don kare kawunansu," kamar yadda takardar ta nuna.

Zamfara: CDS Irabor ya Kalubalanci Umarnin Gwamna ga 'Yan Jihar na Mallakar Makamai

A wani labari na daban, shugaban ma'aikatan tsaro, Janar Lucky Irabor, a ranar Litinin, ya kalubanci kira da gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya yi ga mutanen jihar da su mallaki bindigogi don kare kawunansu daga farmakin 'yan bindiga.

Vanguard ta ruwaito cewa, Irabor ya ce kiran bai dace ba, saboda akwai jami'an tsaro da sauran hukumomin tsaro a wajen don magance matsalar.

Kara karanta wannan

Zamfara: 'Yan Bindiga Sun Kone Ofishin 'Yan Sanda, Shaguna da Gidaje a Bukkuyum

Asali: Legit.ng

Online view pixel