Zan maka Buhari kotu in ya ki tsayawa takarar tazarce a 2019 - Gudaji Kazaure
- Zan maka Buhari kotu in ya ki tsayawa takarar tazarce a 2019 - Gudaji Kazaure
- Dan majalisar ya bayyana hakan ne a yayin wata fira da yayi da gidan rediyon BBC Hausa
- ya ce shi tuni har ma ya fadawa shugaban kasar hakan
Fitaccen dan majalisar wakillan nan dake wakiltar mazabar Kazaure, Roni, Gwiwa da kuma 'Yankwashi watau Honorable Gudaji Kazaure ya sha alwashin sai ya kai Buhari kotu idan har ya kuskura yaki tsayawa takarar tazarce a zaben 2019 mai zuwa.
KU KARANTA: Ba alkalai kudi ba laifi bane - Wani babban Lauya
Dan majalisar ya bayyana hakan ne a yayin wata fira da yayi da gidan rediyon BBC Hausa a satin da ya gabata inda ya bayyana cewa akan shugaba Muhammadu Buhari kam, shi ba gudu ba ja da baya.
Legit.ng ta samu cewa dan majalisar ya ce shi tuni har ma ya fadawa shugaban kasar hakan a wata haduwa da suka yi a watannin baya inda kuma yace yanzu abunda shugaban yake bukata shine cikakken goyon bayan dukkan al'ummar kasar.
A cewar sa, dole ne sai an sha wuya sannan za'a sha dadi kuma tabbas shugaban kasar ya dauko hanyar gyaran kasar musamman ma yadda ya taras da ita ba kudi amma duk da haka komai na tafiya dai dai.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng