Da Dumi-Ɗumi: Kotu ta ba da Belin Ɗan Majalisar tarayya bayan shafe kwanaki 62 a tsare

Da Dumi-Ɗumi: Kotu ta ba da Belin Ɗan Majalisar tarayya bayan shafe kwanaki 62 a tsare

  • Ɗan majalisar tarayya, Honorabul Farah Dagogo, ya samu nasarar samun Beli daga Kotu bayan shafe dogon lokaci a tsare
  • Dagogo, wanda ke fama da shari'a kan zargin aikata babban laifi a jihar Ribas, ya nemi takarar gwamna karkashin PDP
  • An kama ɗan majalisar ne a wurin tantance yan takarar PDP awanni bayan gwamna Wike ya ayyana nemansa

Rivers - Bayan kwashe kwanaki 62 a garkame, Babbar Kotun jihar Ribas karkashin jagorancin Mai Shari'a Chinwendu Nworgu ta amince da buƙatar ba da Belin ɗan majalisar wakilan tarayya, Honorabul Farah Dagogo.

Ledership ta ruwaito cewa Dagogo,wanda ya nemi takarar gwamna a jam'iyyar Peoples Democratic Party wato PDP, na fuskantar shari'a ne kan zargin aikata babban laifi.

Ɗan majalisar ya shiga hannun hukumomi ne a ranar 22 ga watan Afrilu, 2022 a wurin taron tantance yan takarar gwamnan na jam'iyyar PDP wanda ya gudana a Patakwal.

Farah Dagogo.
Da Dumi-Ɗumi: Kotu ta ba da Belin Ɗan Majalisar tarayya bayan shafe kwanaki 62 a tsare Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

An kama shi ne ƙasa da awanni huɗu bayan gwamna Nyesom Ezenwo Wike na jihar Ribas, ya ayyana shi a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo bisa zargin ɗakko hayar yan daba da ake zargin ƴan asiri ne su tarwatsa taron tantancewa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bayan rashin nasara a yunkurin nemar masa yanci lokuta da dama, Mai Shari'a Chinwendu Nworgu, ya yanke hukunci kan bukatar ba da belinsa, wanda Lauyan dake kare shi, Cosmos Enweluzo, SAN, ya shigar.

Sharuddan da ke cikin Belin

Nworgu ya amince da bukatar bayar da belinsa kan kudi miliyan N20m tare da mutum ɗaya da zai tsaya masa kuma ya aje Fasfonsa, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Alƙalin ya ba da umarnin cewa ɗan majalisar ba zai fita ƙasar nan ba har sai Kotu ta amince masa kuma ya kamata ya aje Fastonsa na ƙasa da ƙasa a Kotun.

Ya kuma ƙara da cewa wanda zai tsaya masa wajibe ya zama ɗan asalin jihar Ribas, wanda ya mallaki kadarar ƙasa da takai darajar aƙalla miliyan N20m.

A wani labarin na daban kuma Tsohon ɗan takarar gwamna da wani babban jigon PDP sun sauya sheka zuwa NNPP mai kayan daɗi

Yayin da yan siyasa ke cigaba da tashi daga nan zuwa can, jam'iyyar NNPP mai kayan marmari ta yi babban kamu a jihar Kwara.

Tsohon ɗan takarar gwamna da ɗan uwan tsohon shugaban majalisar Dattawa sun sauya sheka daga jam'iyyun su zuwa NNPP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel