Za a shirya wasan kwaikwayo a kan tarihin tsige Sanusi I da Sanusi II a 1963 da 2020

Za a shirya wasan kwaikwayo a kan tarihin tsige Sanusi I da Sanusi II a 1963 da 2020

  • Kamfanin Duke of Shomolu Productions zai shirya wasan kwaikwayo na tarihin Sarakunan Kano
  • Farfesa Ahmed Yerima zai bada umarni wajen shirya wasan din da za a fitar a watan Agustan 2022
  • Ana sa rai Mai martaba Khalifa Muhammadu Sanusi II ya samu halartar wannan shirin da za a nuna

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Lagos - Shugaban kamfanin shirya wasanni na Duke of Shomolu Productions, Mista Joseph Edgar ya na kokarin ganin matasa sun san tarihin kasar su.

Vanguard ta rahoto Joseph Edgar yana mai kokawa a kan yadda mutane musamman matasa a Najeriya suka manta da abubuwan da suka faru a baya.

Edgar wanda ya kware wajen harkar shirya fina-finai da wasannin kwaikwayo na tarihi ya shaidawa manema labarai cewa jahilci ya kai intaha a yau.

A cewar sa, idan har ana so a san inda aka dosa a Najeriya, ya zama dole a samu tarihin abin da aka yi a baya, abin da ya ce mutanen yau sun rasa sosai.

An manta tarihi a yau

Hukumar dillacin labarai na kasa ta rahoto Joseph Edgar yana bayanin yadda mutane suka shagala da kafofin yanar gizo, suka yi watsi da tarihinsu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mai shirya fina-finan ya bada misali da cewa mafi yawan matasan da ke Legas, ba su da labarin Marigayi Lateef Jakande wanda ya yi gwamna a 1979-83.

Sanusi II
Muhammadu Sanusi II a lokacin hawan Sallah Hoto: insidearewa.com.ng
Asali: UGC

A dalilin haka ake yunkurin shirya wasanni a kan tarihin kasa domin a fadakar da manyan gobe.

Mista Edgar ya ce sun taba yin wasa a game da tsohon Firimiyan kasar Yarbawa Obafemi Awolowo (Awo) da tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo.

Za ayi wasa a kan Sanusi I, II

A watan Agusta 2022, Duke of Shomolu Productions za su shirya wasu jeringiyan wasanni kan labarin tsofaffin Sarakunan Kano, Muhammadu Sanusi I da na II.

A cewar Edgar, ba a fahimci wadannan Sarakuna ba musamman a wajen Kano, don haka za su shirya fim da nufin fitowa Duniya da gaskiyar labarin tunbuke su.

Tsige Mai martaba Sanusi I a 1963 da jikansa, Sanusi II a 2020 ya jawo abubuwa da-dama, don haka za a fito da wannan kayattaccen shiri ga masu sha’awar tarihi.

Za a haska wasannin ne a garuruwan Legas da Abuja tare da shirin tarihin Marigayiya Ladi Kwali. Rahoton ya ce Khalifa Sanusi II zai halarci wannan wasa.

2023: Sanusi II yana tare da Obi?

Kwanakin baya kun ji labari tsohon Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II ya ce sam bai da hannu a wani rubutu kan ‘yan takaran 2023 da mutane ke yadawa.

Mai martaba Muhammadu Sanusi II ya musanya wannan a wani jawabi da ya fitar ta hannun hadiminsa, Malam Munir Sunusi Bayero, ya ce ba da alkalaminsa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel