Yan Sanda Sun Kwato Wasu Motocci Da Aka Sace Daga Najeriya Aka Kai Su Jamhuriyar Nijar

Yan Sanda Sun Kwato Wasu Motocci Da Aka Sace Daga Najeriya Aka Kai Su Jamhuriyar Nijar

  • Jami'an yan sandan Najeriya tare da hadin gwiwar yan sandan Interpol sun yi nasarar kwato wasu motoccin sata a Najeriya
  • Motoccin guda uku an sace su ne daga Najeriya sannnan aka tafi da su Jamhuriyar ta Nijar domin a sayar da su
  • Babban Sufetan Yan Sandan Najeriya, IGP Usman Baba, ya yaba wa yan sandan na Najeriya da kuma Interpol bisa nasara da hadin gwiwa

Jami'an yan sandan Najeriya da hadin gwiwar yan sandan kasa da kasa ta Interpol sun yi nasarar kwato wasu motocci da aka sace daga Najeriya a Jamhuriyar Nijar.

Mai magana da yawun yan sandan Najeriya, Olumuyiwa Adejobi ne ya sanar da hakan, The Punch ta rahoto.

Yan sanda
Yan Sanda Sun Kwato Wasu Motocci Da Aka Sace Daga Najeriya Aka Kai Su Nijar. @MobilePunch.
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Kaduna: Yan Sanda Sun Bindige Dan Ta'adda Har Lahira, Sun Kwato Bindiga Da Babur

Jawabin IGP na Yan sandan Najeriya

Ya ce:

"Sifeta Janar na yan sandan Najeriya, Usman Baba, ya yaba wa hadin gwiwa tsakanin kasashe 194 na yan sanda masu yaki da laifuka na kasa da kasa wacce ta taimaka wurin yaki da laifuka a duniya.
"IGP din har wa yau ya yaba wa sashin binciken manyan laifuka, saboda amfani da bayanai da suka samu a hannun INTERPOL don dakile laifukan kasa da kasa musamman abin da ya shafi kasashen Afirka da muke makwabtaka da su.
"Ya yi wannan jawabin ne bayan nasarar kwato wasu motocci guda uku da aka sace daga Najeriya aka kai Jamhuriyar Nijar."

EFCC Ta Kama Tsohon Gwamna Da Matarsa Kan Zargin Rashawa

A wani labarin, mun kawo muku cewa Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta kama tsohon gwamnan jihar Nasarawa kuma sanata mai ci a yanzu, Tanko Al-Makura da matarsa kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Layukan Wayan Ekweremadu Da Na Kakakinsa A Kashe, Yayin Da Aka Kama Shi Da Matarsa A Landan

Majiyoyi daga hukumar yaki da rashawar sun shaidawa Premium Times cewa a halin yanzu jami'an EFCC na yi wa tsohon gwamnan da matarsa tambayoyi a hedkwatar ta da ke Abuja.

Duk da cewa ba a samu cikaken bayani kan dalilin kama tsohon gwamnan da matarsa ba, majiyoyi sun ce kamun na da nasaba da zargin cin amana da bannatar da kudade da gwamnan yayi yayin mulkinsa na shekaru takwas a matsayin gwamnan Nasarawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel