Da duminsa: Babban Limamin Masallacin Juma'a a Kaduna, Ya Riga mu Gidan gaskiya

Da duminsa: Babban Limamin Masallacin Juma'a a Kaduna, Ya Riga mu Gidan gaskiya

  • Malam Dahiru Lawal ABubakar, babban limamin Masallacin Juma'a na titin Maiduguri dake garin Kaduna ya riga mu gidan gaskiya
  • Alkalin wata babbar kotun shari'a dake karamar hukumar Makarfi ta jihar Kaduna, ya rasu sakamakon gajeriyar rashin lafiya
  • Malamin 'da ne ga fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Lawal Abubakar, kuma ya rasu yana da shekaru 52 a duniya

Kaduna - Babban limamin masallacin Juma'a na titin Maiduguri a cikin garin Kaduna, Malam Dahiru Lawal Abubakar, ya rasu yana da shekaru 52 a duniya.

Daily Trust ta tattaro cewa, babban limamin wanda kafin rasuwarsa, alkali ne a babbar kotun shari'a dake kaamar hukumar Makarfi ta jihar Kaduna, ya rasu sakamakon gajeriyar rashin lafiya.

Kaduna: Babban Limamin Masallacin Juma'a Na Titin Maiduguri, Ya Riga mu Gidan Gaskiya
Kaduna: Babban Limamin Masallacin Juma'a Na Titin Maiduguri, Ya Riga mu Gidan Gaskiya. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Ya yi jinyar a asibtin 44 na sojoji kafin ya rasu a sa'o'in farko na ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Abin Da Sheikh Gumi Ya Ce Kan Rasuwar Alkali Dahiru Lawal Abubakar A Kaduna

Babban limamin 'da ne ga fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Lawal Abubakar, kuma yayan daya daga cikin tsoffin editocin Daily Trust mai suna Malam Nasiru Lawal Abubakar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A Zantawar da Legit.ng ta yi da wani makwabcin masallacin da Malam Dahiru Lawal ke limanci, wanda ya bukaci a boye sunansa, ya sanar da cewa Malam mutum ne nagari kuma ana sa masa ran rahamar Ubangiji.

Ya bayyana yadda Malam yake kan gaba a duk lamurran da suka shafi addinin Musulunci tare da nagartattun halayensa.

"Koda barewa bata gudu 'dan ta yayi rarrafe, babu shakka za mu ce ya gaji mahaifinsa ne wanda suka yi makwabtaka da mahaifina. Kafin rasuwar mahaifina, in har zai yi misalin kyakyawar alaka da dabi'a ta 'dan Adam, Malam Lawal Abubakar yake fara kawowa matsayin misali. Allah ya gafarta masa, yasa duka sun huta," yace.

Kara karanta wannan

Tsohon Shugaban Najeriya ya samu sauki bayan ya kwanta jinya a asibitin kasar waje

Fitaccen Farfesa na BUK, Emmanuel Ajayi Olofin, ya Riga mu Gidan Gaskiya

A wani labari na daban, wani fitaccen Farfesan ilimin Jogirafi a jami'ar Bayero dake Kano (BUK), Emmanuel Ajayi Olofin ya riga mu gidan gaskiya. Marigayin, 'dan asalin Ijero cikin jihar Ekiti ya rasu a ranar Talata yana da shekaru 80, Daily Trust ta ruwaito.

Kafin mutuwarsa, Olafin ya koyar a fannin jogirafi a BUK, inda ya kai kololuwa a fannin.

Ya yi karatu da jami'ar Ibadan, inda ya yi digirinsa na farko a fannin Jogirafi, digirin-digir a jami'ar Malaya dake Malaysia sannan ya zarce jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria inda ya yi digirin-digirgir.

Ya koyar a makarantun gaba da sakandiri da dama wadanda suka hada da jami'ar Najeriya ta Nsukka, jami'ar Obafemi Awolowo ta Ife, jami'ar Malaya da kuma jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel