Abin Da Sheikh Gumi Ya Ce Kan Rasuwar Alkali Dahiru Lawal Abubakar A Kaduna

Abin Da Sheikh Gumi Ya Ce Kan Rasuwar Alkali Dahiru Lawal Abubakar A Kaduna

  • Sheikh Gumi ya bayyana rasuwar babban limamin masallacin Maiduguri Road a Kaduna, Alkali Dahiru Lawal Abubakar a matsayin babban rashi ga al'ummar musulmi
  • Gumi ya ce yana damuwa duk lokacin da malami ya rasu domin maye gurbinsa kallubale ne kuma malamai ke daidaita al'umma da karantar da su
  • Malam Nasiru Lawal Abubakar, kanin marigayin, ya bayyana shi a matsayin mahaifi yana mai cewa ya maye gurbin mahaifinsu a matsayin babban limamin masallaci

Kaduna - Fitaccen malamin addinin musulunci, Dr Ahmad Gumi ya bayyana rasuwar babban limamin masallacin Maiduguri Road a Kaduna, Alkali Dahiru Lawal Abubakar a matsayin babban rashi ga al'ummar musulmi a jihar.

Daily Trust ta rahoto cewa babban limamin ya rasu ne a ranar Laraba bayan fama da gajeruwar rashin lafiya a Asibitin Sojoji na 44 a Kaduna, yana da shekaru 52, kafin rasuwarsa alkali ne a babban kotun sharia a karamar hukumar Makarfi a jihar.

Kara karanta wannan

Gaskiyar abinda Sanata Ekweremadu da matarsa suka faɗa wa Kotun Landan kan zargin yanke sassan jiki

Shiekh Ahmad Gumi.
Sheikh Gumi: Rasuwar Alkali Dahiru Lawal Abubakar Babban Rashi Ne Ga Al'ummar Musulmi. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Gumi, wanda ya jagoranci sallar jana'izar tare da al'umma da dama, ya ce ya kan damu duk lokacin da malami ya rasu.

Ya ce neman wanda zai maye gurbin malami idan ya mutu babban kalubale ne, "domin suna taimakawa wurin daidaita kasa da ilmantar da al'umma."

Gumi ya ce:

"Dan fitaccen malami ne, marigayi Sheikh Lawal Abubakar. Allah ya gafarta musu ya saka musu da aljanna firdausi baki daya."

Abin da kanin marigayin ya bayyana game da rasuwar malamin

Malam Nasiru Lawal Abubakar, kanin marigayin kuma tsohon Edita ta jaridar Daily Trust, ya bayyana shi a matsayin mahaifi yana mai cewa ya maye gurbin mahaifinsu a matsayin babban limamin masallaci shekaru da suka shude.

"Tamkar mahaifi ya ke a wurin mu kuma ba shine babba a gidan mu ba amma saboda ya maye gurbin mahaifin mu, duk muna ganinsa a matsayin mahaifi. Allah ya saka masa da aljanna firdausi, amin," in ji shi.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Babban Limamin Masallacin Juma'a a Kaduna, Ya Riga mu Gidan gaskiya

Daruruwan mutane sun ziyarci gidan marigayin malamin da ke Maiduguri Road, a karamar hukumar Kaduna North don musu gaisuwa.

Gwamnatin Kaduna Ta Kori Malamai 2,357 Daga Aiki Ciki Har Da Shugaban Kungiyar Malamai NUT

A wani rahoton daban, Hukumar Ilimi Bai Daya na Jihar Kaduna, KADSUBEB, ta ce ta kori malamai 2,357 wadanda suka fadi jarrabawar cancanta da aka gudanar a baya-bayan nan, rahoton Vanguard.

Mai magana da yawun hukumar, Mrs Hauwa Mohammed cikin wata sanar da ta fitar, a ranar Lahadi a Kaduna ta ce hukumar ta yi wa fiye da malamai 300000 gwajin cancantar a watan Disambar 2021.

Asali: Legit.ng

Online view pixel