Fitaccen Farfesa na BUK, Emmanuel Ajayi Olofin, ya Riga mu Gidan Gaskiya

Fitaccen Farfesa na BUK, Emmanuel Ajayi Olofin, ya Riga mu Gidan Gaskiya

  • Wani fitaccen Farfesan Jogirafi na jami'ar Bayero dake Kano, Emmanuel Ajayi Olofin ya rasu yana da shekaru 80 a duniya bayan karatun da ya yi mai zurfin gaske gami da shahara
  • Marigayin 'dan asalin Ijero na jihar Ekiti, ya rasu ranar Talata bayan kai wa kololuwa saboda irin kwazonsa bayan rike mukamai da dama a fannin iliminsa tare da lashe kyautuka da dama
  • Farfesan ya yi digirinsa na farko da na biyu a jami'ar Malaya ta Malaysia daga bisani garzaya ABU inda yayi digirin-digirgir, sannan ya koyar a makarantun gaba da sakandiri da dama

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kano - Wani fitaccen Farfesan ilimin Jogirafi a jami'ar Bayero dake Kano (BUK), Emmanuel Ajayi Olofin ya riga mu gidan gaskiya.

Marigayin, 'dan asalin Ijero cikin jihar Ekiti ya rasu a ranar Talata yana da shekaru 80, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kano: Majalisar Dokoki Amince Ganduje Ya Ciyo Bashin Naira Biliyan 10

Farfesa Emmaneul Ajayi Olofin na jami'ar Bayero dake Kano
Fitaccen Farfesa na BUK, Emmanuel Ajayi Olofin, ya Riga mu Gidan Gaskiya. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kafin mutuwarsa, Olafin ya koyar a fannin jogirafi a BUK, inda ya kai kololuwa a fannin.

Ya yi karatu da jami'ar Ibadan, inda ya yi digirinsa na farko a fannin Jogirafi, digirin-digir a jami'ar Malaya dake Malaysia sannan ya zarce jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria inda ya yi digirin-digirgir.

Ya koyar a makarantun gaba da sakandiri da dama wadanda suka hada da jami'ar Najeriya ta Nsukka, jami'ar Obafemi Awolowo ta Ife, jami'ar Malaya da kuma jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria.

A lokacin rayuwarsa, shi mamba ne a kungiyar masana Jogirafi ta kasashe; mamba na kungiyar masana Jogirafi ta Malayen a shekarar 1970 zuwa 1972 ta turai.

Mamba ne Kungiyar bincike na Jogirafi daga shekarar 1985 zuwa yanzu; mamban kungiyar Jogirafi ta Amurka tun shekarar 1990; mamban dalibi a kungiyar Jogirafi ta Malaysia; Shugaban kungiyar Katolika na yankin Idon Ekiti.

Kara karanta wannan

Kiyayya Ta Makantar Da Kai: Femi Adesina Ya Caccaki Oyedepo Kan Alkanta Gwamnatin Buhari Da Rashawa

Ya ci gasar Commonwealth Scholarship ta Malaysia a shekarar 1970-1972; Gasar USAID ta interfaith Dailogue a shekarar 1991; Kyautar ziyara zuwa Ingila daga Turai a shekarar 1987.

Kamar yadda Legit.ng ta ji daga bakin wani tsohon dalibinsa da ya koyar a matakin digiri na biyu a bangaren kula da muhalli, mai suna Jazuli Aminu, ya sanar da cewa mutumin kirki ne mai halin dattako.

"Wannan rashin ba sashin jogirafi kadai ya shafa ba, ya shafi dukkan jami'ar Bayero. Mutum ne nagari, mai halayyar kirki da dattako. Lallai an yi babban rashi," yace.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel