Kano: Majalisar Dokoki Amince Ganduje Ya Ciyo Bashin Naira Biliyan 10

Kano: Majalisar Dokoki Amince Ganduje Ya Ciyo Bashin Naira Biliyan 10

  • Majalisar Dokokin Jihar Kano ta sahale wa Gwamna Abdullahi Ganduje ya karbo rancen kudi Naira biliyan 10 daga wani banki a Najeriya
  • Yayin karanto wasikar yayin zaman majalisar, kakakin majalisar Hamisu Chidari ya ce gwamnatin na Kano za ta yi amfani da kudin ne don siyo na'urorin inganta tsaro
  • Labaran Madari (APC-Warawa) jagoran majalisar, ya ce dalilin ciwo bashin yana da kyau kuma ana fatan biyan bashin cikin shekaru 10

Jihar Kano - Majalisar Dokoki na Jihar Kano, a ranar Laraba ta amince da bukatar da Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar ya nema na ciyo bashin Naira biliyan 10 daga banki.

Amincewar na zuwa ne bayan kakakin majalisar, Hamisu Chidari ya karanto wasikar yayin zaman majalisar a ranar Laraba, rahoton NAN.

Majalisar Dokoki na JIhar Kano.
Majalisar Dokokin Kano Ta Amince Ganduje Ya Ciyo Bashin N10bn. Hoto: @DailyNigerian
Asali: Twitter

A cewar wasikar, za a yi amfani da kudin ne domin siyo kyamara na tsaro wato CCTV da wasu na'urori da ake bukata don inganta tsaro a jihar.

Kara karanta wannan

Kiyayya Ta Makantar Da Kai: Femi Adesina Ya Caccaki Oyedepo Kan Alkanta Gwamnatin Buhari Da Rashawa

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Da ya ke magana kan batun, jagoran majalisar, Labaran Madari (APC-Warawa) ya ce dalilin ciwo bashin yana da kyau.

Ya ce ruwa da ke tattare da bashin babu yawa kuma za a iya biya cikin shekaru 10.

Mr Madari ya ce za a yi amfani da kudin don gina dakunan tattara bayanai na tsaro da bayannan sirri.

"Za a saka na'urorin a hedkwatar masarautu biyar na jihar.
"Dalilin hakan shine inganta tsaro da dakile aikata laifuka a jihar," in ji shi.

Dukkan yan majalisan suka hallarci zaman majalisar sun amince da bukatar ciyo bashin.

2023: Atiku Ya Bayyana Manufofi 5 Da Zai Yi Amfani Da Su Don Tsallakar Da Najeriya Zuwa Ga Tudun Mun Tsira

A wani rahoton, dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP kuma tsohon mataimakin shugaban kasa ya saki burikansa biyar wadanda ya ke son cikawa da zarar an zabe shi a matsayin shugaban kasa.

Kara karanta wannan

An Kori Lakcarorin Najeriya 2 Saboda Tafka 'Manyan' Laifuka a Jami'a

Ya saki kudirorin nasa guda biyar ne ta shafinsa na Twitter yayin da ake shirye-shiryen zaben fidda gwanin jam’iyyar PDP a karshen makon nan.

Atiku, dan takarar da ya tsaya karkashin inuwar PDP a zaben 2019 ya yi alkawarin kawo karshen rashin tsaro, tabarbarewar tattalin arziki da sauran matsalolin da su ka addabi kasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel