2023: Atiku Ya Bayyana Manufofi 5 Da Zai Yi Amfani Da Su Don Tsallakar Da Najeriya Zuwa Ga Tudun Mun Tsira

2023: Atiku Ya Bayyana Manufofi 5 Da Zai Yi Amfani Da Su Don Tsallakar Da Najeriya Zuwa Ga Tudun Mun Tsira

  • Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, a ranar Laraba ya saki kudirorinsa guda 5 da ya ke shirya wa Najeriya idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa
  • Atiku, wanda dan takarar shugaban kasa ne karkashin jam’iyyar PDP ya saki kudirorin nasa ta shafinsa na Twitter yayin da ake shirin yin zaben fidda gwanin jam’iyyar a karshen mako
  • A cewarsa burinsa na farko shi ne dawo da hadin kan Najeriya ta hanyar adalci da kawo hadin kai sai kuma shigabanci na kwarai da tsaron rayuka da sauransu

A ranar Laraba, dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP kuma tsohon mataimakin shugaban kasa ya saki burikansa biyar wadanda ya ke son cikawa da zarar an zabe shi a matsayin shugaban kasa.

2023: Atiku Ya Bayyana Manufofi 5 Da Zai Amfani Da Su Don Tsallakar Da Najeriya Zuwa Ga Tudun Mun Tsira
2023: Atiku Ya Bayyana Manufofi 5 Da Zai Amfani Da Su Don Ceto Najeriya. Hoto: Atiku Abubakar.
Asali: Twitter

Ya saki kudirorin nasa guda biyar ne ta shafinsa na Twitter yayin da ake shirye-shiryen zaben fidda gwanin jam’iyyar PDP a karshen makon nan.

Kara karanta wannan

Kano: Kotu jaddada Shehu Sagagi, na hannun daman Kwankwaso a matsayin shugaban PDP

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Atiku, dan takarar da ya tsaya karkashin inuwar PDP a zaben 2019 ya yi alkawarin kawo karshen rashin tsaro, tabarbarewar tattalin arziki da sauran matsalolin da su ka addabi kasar nan.

Ga dai kudirorin kamar yadda ya lissafo su

1. Dawo da hadin kai Najeriya ta hanyar daidaito, adalci da hada kan al'umma.

2. Kafa gwamnati nagari wacce za ta tabbatar da tsaron rayyuka da dukiyoyin al'umma.

3. Kafa tattalin arziki mai nagarta wanda zai samar da ayyukan yi tare da ciro mutanen mu daga talauci.

4. Tabbatar da kafa gwamnatin tarayya ta ainihi wacce za samar da gwamnatin tarayya kwakwara da hadin kai tsakanin bangarorin tare da basu daman fifita abin da suka fi so.

5. Yin garambawul a bangaren ilimi ta hanyar kirkire-kirkire, kimiyya da fasaha.

Kara karanta wannan

Sabon rikici ya kunno kai a APC reshen Kaduna, surukin Buhari bai aminta da deleget din jam’iyyar ba

'Batanci: Atiku Ya Ce Ba Shine Ya Wallafa Rubutun Sukar Kashe Ɗalibar Sokoto a Shafinsa Ba

A wani rahoton, Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP ya nisanta kansa daga yin ala-wadai akan kisan Deborah Samuel.

Deborah dalibar aji biyu ce a kwalejin ilimi ta Shehu Shagari da ke Jihar Sokoto, kuma kirista ce, an halaka ta ne bisa zarginta da yin batanci ga Annabi Muhammad SAW.

Sai dai Atiku ya yi wata wallafa a Twitter inda ya ce:

“Babu adalci dangane da kisan muguntar da aka yi mata. An halaka Deborah Yakubu kuma wajibi ne a kwatar mata hakkinta akan wadanda su ka halaka ta. Ina mai yi wa ‘yan uwanta da kawayenta ta’aziyya.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel