Shugaban EFCC Ya Bayyana Hanya Mafi Sauki Da Barayin Gwamnati Ke Boye Kudadensu a Najeriya

Shugaban EFCC Ya Bayyana Hanya Mafi Sauki Da Barayin Gwamnati Ke Boye Kudadensu a Najeriya

  • Abdulrasheed Bawa, Shugaban Hukumar Yaki Da Rashawa ta EFCC ya ce mafi yawancin masu satar kudade a Najeriya filaye da gidaje suke siya don boye kudin
  • Bawa ya bayyana hakan ne yayin da shugaban kungiyar kwararrun dillalan gidaje da filaye na aksa, NIESV, da mambobinsa suka kai masa ziyara a ofishinsa da ke Abuja
  • Shugaban na hukumar yaki da rashawar ya bada misalin wani tsohon ma'aikacin gwamnati wanda ya gina jami'a a Kaduna da kudin sata kuma hukumar ta NIESV bata ankarar da EFCC ba kamar yadda doka ta tanada

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Shugaban hukumar yaki da rashawa da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati, EFCC, Abdulrasheed Bawa, ya ce siyan gidaje da filaye hanya ce mai sauki da masu satar kudi ke boye dukiyoyinsu.

Daily Trust ta rahoto cewa ya furta hakan ne a jiya a Abuja a lokacin da ya karbi bakuncin Shugaban Kungiyar Kwararru masu dillancin gidaje da filaye, (NIESV), Emmanuel Wike.

Shugaban EFCC Ya Bayyana Hanya Mafi Sauki Da Barayin Gwamnati Ke Boye Kudadensu a Najeriya
Shugaban EFCC: Siyan gidaje da filaye ne hanya mafi sauki da masu satar kudi ke boye kudadensu. Hoto: @daily_trust.
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Wata daya da ya wuce, mun gano cewa wani ma'aikacin gwamnati da ya yi ritaya ya gina Jami'a a Kaduna kuma babu wanda ya sanar da mu, har mambobin ku.
"Don haka, ba zan yi shakkan cewa siyan filaye da gidaje yana daya daga cikin hanyoyi mafi sauki na boye kudi ga masu sata. Shi yasa za mu karfafa SCUML da dukkan kayan aiki don taimaka mana sauke nauyin da ke kanmu, duk abin da muke yi doka ta amince da shi, " in ji shi.

Ya bukaci mambobin kungiyar ta NIESV su rika biyayya ga dokar aikinsu na sanar da EFCC duk wani ciniki ko hada-hada kamar yadda ya ke a dokar hana almundahar kudade na 2022.

A bangarensa, Wike ya EFCC ta taka rawar a zo a gani wurin gurfanar da manyan mutane da ke aikata rashawa.

Ya bada tabbacin cewa mambobinsa za su bawa EFCC hadin kai wurin tona asirin bara-gulbi a cikinsu.

Ahmed Idris: EFCC Ta Sako Dakataccen Akanta Janar Da Ake Zargi Da Wawure N170bn

A wani rahoton, hukumar Yaki da Rashawa da Masu Yi Wa Arzikin Kasa Ta'annati, EFCC, ta sako dakataccen Akanta Janar na kasa, Ahmed Idris da ta kama kwanakin baya, Daily Nigerian ta rahoto.

Wasu majiyoyi daga iyalan Ahmad sun tabbatarwa Daily Nigerian da sakinsa inda suka ce a daren ranar Laraba aka sako shi.

Jami'an hukumar EFCC, a ranar 16 ga watan Mayu ne suka kama Mr Idris kan zarginsa da hannu wurin karkatar da kudade da adadinsu ya kai Naira Biliyan 80.

Asali: Legit.ng

Online view pixel