Kaduna: Gobara ta tashi a kwalejin ilimi ta Zaria, ta barnata kwamfutoci 100
- An samu tashin gobara a kwalejin ilimi ta Zaria, inda aka ruwaito lalacewar kwamfutoci da dama a gobarar
- Rahoto ya bayyana cewa, gobarar da aka sha faman kashewa ta lalata kwamfutoci 100, kana ta kone wani sashen makarantar
- Shugaban kwalejin ya bayyana yadda lamarin ya faru tare da bayyana matakin da kwalejin ta dauka na wuccin gadi
Zaria, Kaduna - Sama da kwamfutoci 100 ne suka lalace a wata gobara da ta tashi a Sashen Kwamfuta na Kwalejin Ilimi ta Tarayya da ke Zaria a Jihar Kaduna, rahoton Daily Trust.
Jami’an kashe gobara sun dauki tsawon lokaci suna gwabzawa domin shawo kan gobarar da ta tashi da misalin karfe 9 na safiyar ranar Asabar lokacin da ma’aikata ba sa wurin aiki.
Shugaban kwalejin, Dakta Suleiman Balarabe, ya ce gobarar ta tashi ne daga wata na'urar hana katsewar wutar lantarki (UPS).
Ya ce doka ce a kwalejin cewa dole ne a kashe dukkan na’urorin wutar lantarki bayan sa’o’in aiki, yana mai tabbatar da cewa za a sauya kwamfutocin.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya kuma ce an dauki matakan hana sake afkuwar lamarin.
Ya kara da cewa:
“Zan kuma fitar da wasu kwamfutoci da TETFUND ta baiwa kwalejin a baya da kuma samar da wurin wucin gadi don amfani da su domin baiwa dalibai damar ci gaba da gudanar da harkokin ilimi har zuwa lokacin da za a gyara ginin da ya kone.
"Dole in yi godiya ga kokarin ABU Kongo da ma'aikatan kashe gobara na jihar Kaduna da suka kawo mana dauki cikin gaggawa lokacin da gobarar ta tashi."
Legit.ng Hausa ta tuntubi wata dalibar bangaren digiri a kwalejin, Aishatu Usman ta kuma shaida cewa:
"Ginin ya kone sosai, yau Litinin da na zo na ga wurin ba yadda yake, amma an kwashe abubuwan ciki. Da alamu kuma za a fara aikin gyara, domin na ga wasu suna zirga-zirga a wurin, kuma kamar ba dalibai bane.
"Mukan shiga barayin domin rubuta jarrbawa wasu lokutan, kuma zan iya cewa dalibai za su yi kewarsa saboda akwai natsuwa sosai gashi babu hayaniyar jama'a."
Tsohon shugaban kwalejin ilimi (FCE) ta Zariya, Dr. Ango A. Ladan ya rasu
A wani labarin, Babban jami'in kwalejin ilimi na tarayya (FCE) dake Zariya, Dr Ango A. Ladan, ya rasu da safiyar Litinin da misalin karfe 3 na safe, a cewar majiya.
Magatakardar kwalejin, Dokta Jibril Lawal, ya tabbatar da mutuwar a cikin wani sakon tes, yana mai cewa an shirya yin sallar jana’izar mamacin da misalin karfe 2:30 na ranar Litinin a gidan dangin Dr Ladan da ke Unguwan Juma, cikin garin Zariya.
Daily Trust ta ruwaito cewa wa’adin farko na Dr Ladan a kwalejin ilimi na Zariya ya kare ne a ranar 4 ga Fabrairun 2021.
Asali: Legit.ng