Tsohon shugaban kwalejin ilimi (FCE) ta Zariya, Dr. Ango A. Ladan ya rasu

Tsohon shugaban kwalejin ilimi (FCE) ta Zariya, Dr. Ango A. Ladan ya rasu

- Tsohon shugaban kwalejin ilimi ta Zariya (FCE) ya rasu da safiyar ranar Litinin 8 ga watan Fabrairu

- Majiya ta tabbatar da rasuwar tsohon shugaban da cewa ya rasu da misalin karfe 3 na safe

- Za a yi jana'izar tsohon shugaban da misalin karfe 2:30 na safe a unguwar Juma cikin Zariya

Babban jami'in kwalejin ilimi na tarayya (FCE) dake Zariya, Dr Ango A. Ladan, ya rasu da safiyar Litinin da misalin karfe 3 na safe, a cewar majiya.

Magatakardar kwalejin, Dokta Jibril Lawal, ya tabbatar da mutuwar a cikin wani sakon tes, yana mai cewa an shirya yin sallar jana’izar mamacin da misalin karfe 2:30 na ranar Litinin a gidan dangin Dr Ladan da ke Unguwan Juma, cikin garin Zariya.

KU KARANTA: Rudani yayin da sojoji suka gano kayan sojoji, katin shaida na sojoji 145 a Borno

Tsohon shugabab kwalejin ilimi (FCE) na Zariya, Dr. Ango A. Ladan ya rasu
Tsohon shugabab kwalejin ilimi (FCE) na Zariya, Dr. Ango A. Ladan ya rasu Hoto: FCE Zaria
Asali: Twitter

Daily Trust ta ruwaito cewa wa’adin farko na Dr Ladan a kwalejin ilimi na Zariya ya kare ne a ranar 4 ga Fabrairun 2021.

Sai dai, Gwamnatin Tarayya ba ta sabunta nadin nasa ba a karo na biyu kuma ba a hukumance ta nada mai rikon kwarya na mukamin ba.

Wannan ya haifar da damuwa da firgici a kwalejin, duk da cewa Mataimakin shugaban din, Dr Suleiman Balarabe ne, a yanzu haka yake jagorantar al'amuran makarantar.

KU KARANTA: Watakila mace ta gaji kujerar shugaba Buhari a zaben 2023, Zainab Marwa

A wani labarin, Mai martaba Sarkin Karaga na jihar Neja, Alhaji Salihu Tanko ya rasu, The Nation ta ruwaito. Tsohon Sanatan Kaduna, @ShehuSani ya tabbatar da rasuwar Sarkin a shafinsa na twitter a ranar Talata.

Ya ce, “Na samu labarin bakin ciki game da rasuwar Sarkin Kagara na Jihar Neja, Alhaji Salihu Tanko. Allah Ya ba shi gidan Aljanna firdausi. Amin. Inna lillahi wainna Illayhir rajiun.” An nada Salihu Tanko a matsayin Sarki na 16 na Tegina a 1971.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel