Yajin Aiki: Fitaccen Mai Gabatar Da Shirye-Shirye a Rediyo Zai Tara Wa ASUU N18bn Don Su Koma Aji

Yajin Aiki: Fitaccen Mai Gabatar Da Shirye-Shirye a Rediyo Zai Tara Wa ASUU N18bn Don Su Koma Aji

  • Ahmed Isah, fitaccen mai rajin kare hakkin bil adama kuma mai gabatar da shirye-shirye a rediyo ya kaddamar ya shirin tara wa ASUU N18bn don su koma aji
  • Kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis ya ce ba dole bane sai Najeriya ta ciwo bashi daga kasashen waje domin warware matsalolinta
  • Ya yi kira ga yan Najeriya masu taro da sisi da su bad tallafi saboda yara a Najeriya su koma makaranta

Fitaccen mai rajin kare hakkin bil adama, kuma mai gabatar da shirye-shirye, Ahmed Isah, da aka fi sani da Ordinary President ya kaddamar da kamfen don tara wa kungiyar malaman jami'o'i, ASUU, Naira Biliyan 18 don su koma aji.

Yajin Aiki: Fitaccen Mai Gabatar Da Shirye-Shirye a Rediyo Zai Tara Wa ASUU N18bn Don Su Koma Aji
Yajin Aiki: Fitaccen Mai Gabatar Da Shirye-Shirye a Rediyo, Ahmed Isah, Zai Tara Wa ASUU N18bn Don Su Koma Aji. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Ba za a ba Abduljabbar Kabara lauya a kyauta ba – Lauyoyin jihar Kano sun kawo dalilinsu

Isah ya kaddamar da kamfen din neman tallafin ne ga ASUU a shirin Berekete Family na musamman da aka sadaukar saboda yajin aikin ASUU kamar yadda Legit.ng Hausa ta gano ya kuma wallafa a shafinsa na Twitter.

Ya jadadda cewa ba dole sai Najeriya ta ciyo bashi ba daga kasashen ketare, yana mai cewa kasar tana da kudin da za ta iya kula da kanta.

"Ina fada muku ya zama dole yaran mu su koma makaranta. Babu bukatar Najeriya ta karbo bashin kudi daga kasashen waje, muna da isasun kudi," Isah ya rubuta a shafinsa na Twitter.

Ya cigaba da cewa:

"Wannan tallafin da za mu yi domin ASUU manuniya ne kan yadda za mu sauya abubuwa a kasar nan. Kudin ka 50, 100, 200, 300, 400, ko 500 zuwa Naira Biliyan 1, zai yi tasiri. Me ka ke jira? Don Allah, yan Najeriya ku tabbatar kun taimaka.

Kara karanta wannan

Deliget din PDP ya sadaukar da dukkan kudin da ya samu ga al'ummarsa, ya biya wa yara kudin makaranta

"Ba abin kunya bane ka tallafawa mahaifinka da mahaifiyarka. Za mu tallafawa Gwamnatin Tarayya. Mu saka baki, mu tara 18 biliyan don taimakawa mu kare karshen #ASUU Strike."

Kungiyar malaman jami'o'in ta fara yajin aikin ne tun ranar 14 ga watan Fabrairun shekarar 2022 kan wasu yarjejeniya da Gwamnatin Tarayyar Najeriya bata cika mata ba.

An yi ta zama na sulhu amma kawo yanzu ba a cimma matsaya na janye yajin aikin ba.

Yajin Aikin ASUU: Ba Za Mu Bar Titunan Abuja Ba Har Sai An Buɗe Makarantu, 'Kungiyar NANS

A wani rahoto, Kungiyar Daliban Najeriya, NANS, a ranar Litinin ta cigaba da zanga-zangar ta na neman ganin an kawo karshen yakin aikin da kungiyar malaman jami'o'i, ASUU, ke yi.

Da ya ke magana a yayin zanga-zangar a Abuja, shugaban NANS na kasa, Sunday Asefon, ya ce daliban a shirye suke su fito su mamaye manyan titunan Abuja, rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

Dan Najeriya Da Ya Yi Digiri a Jami'ar Harvard Ta Birtaniya Ya Bayyana Sadaukarwar Da Iyayensa Suka Yi Don Tura Shi Karatu

Ya kara da cewa daliban sun gaji kuma ba za su fasa abin da suka fara ba har zai an bude dukkan jami'o'i a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel