Dan Najeriya Da Yayi Digiri a Harvard Ta Birtaniya Ya Fadi Sadaukarwar Da Iyayensa Suka Yi Don Tura Shi Karatu

Dan Najeriya Da Yayi Digiri a Harvard Ta Birtaniya Ya Fadi Sadaukarwar Da Iyayensa Suka Yi Don Tura Shi Karatu

  • Wani dan Najeriya mai suna Temitope Akande ya nuna takardar shaidan kammala karatunsa a intanet tare da bayyana sadaukarwar da iyayensa suka masa
  • Mutumin, wanda ya kammala karatu a Jami'ar Harvard ya wallafa hotunsa tare da iyayensa a gaban shagonsu na sayar da littafai yana cewa shagon ne ya raine shi
  • Labarin Temitope ya karfafa wa mutane da dama gwiwa a LinkedIn inda ya wallafa labarin suka kuma rika san barka suna taya shi murna

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Temitope Akande, wani dan Najeriya da ya kammala karatu a Jami'ar Harvard ya yi wa iyayensa godiya bisa sadaukarwar da suka masa a rayuwarsa.

Ya wallafa wani hotonsa tare da iyayensa mai karfafa gwiwa a gaban shagonsu na sayar da littfai yana mai cewa shagon ne ya raine shi.

Dan Najeriya Da Yayi Digiri a Harvard Ta Birtaniya Ya Fadi Sadaukarwar Da Iyayensa Suka Yi Don Tura Shi Karatu
Dan Najeriya Da Ya Yi Digiri a Harvard Ya Fadi Sadaukarwar Da Iyayensa Suka Yi Don Tura Shi Karatu. Hoto: Photo credit: LinkedIn/Temitope Akande.
Asali: UGC

Ba zan iya ba idan ba domin taimakon iyaye na ba

Kara karanta wannan

Gwamna Wike: Da Na So, Da Na Tarwatsa Jam'iyyar PDP a Daren Asabar, Hakuri Kawai Nayi

Hoton da aka dauka a gaban karamin shagon sayar da littafan ya dauki hankulan mutane da dama a LinkedIn inda Temitope ya wallafa labarinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rufin shagon ya fara tsatsa ga kuma kura amma duk da hakan matashin yana alfahari da shagon saboda taimaka masa cimma burinsa na karatu.

Da ya ke bada labarin, Temitope ya rubuta:

"Ba mu taso cikin kudi ko gata ba, wani matashin talakan yaro ne daga Agbado, amma kuma mun yi nasara daga karshe.
"Ba domin wadannan mutanen biyu masu kirki ba, da ban cimma buri na ba musamman mahaifiyata! Ita ce jaruma ta! Wannan shagon da ke bayan ne ya raine ni.
"Shagon ya bamu abinci, kuma a nan na ke shafe awanni ina karanta littafai, ina karanta abubuwan da ke wasu kasashen duniya kuma hakan ya karfafa min gwiwa. Yau, na yi digiri a Jami'o'in Wharton da Harvard. Ina godiya sosai!".

Kara karanta wannan

Ni ne nan namijin duniya: Wani bakin fata ya saki hotunan yara 33 da ya haifa da yan mata daban-daban

Masu amfani da shafin LinkedIn sun tofa abarkacin bakinsu

Akinmolayan Fisayo ya ce:

"Ina taya ka murna Temitope Akande. Na saba siyan littfai a shagon mamanka a Agbado. Ban taba sanin unguwar mu daya ba. Allah ya yi wa iyayenka da kai albarka. Labarin ka mai karfafa gwiwa ne ga daliban ilimi!!!."

Kola Fatokun ya ce:

"Ba za mu iya kwatanta taimakon da iyaye ke mana ba, kuma ba za mu iya biyansu ba. Amma, a kowanne lokaci, ya kamata mu rika alfahari da su. Nagode da wallafa wannan labarin."

Bayan rayuwa cikin daji yana cin ciyawa, yanzu wankan sutturu na alfarma ya ke yi, ana girmama shi a gari

A wani rahoton, wani matashi, Nsanzimana Elie ya kasance a baya ya na zama cikin daji saboda yanayin suffar sa, sannan mutanen kauyen sa har tonon sa su ke yi.

Akwai wadanda su ke kiran sa da biri, ashe daukaka ta na nan biye da shi, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Mutumin da ya so kashe kansa ya samu kyautar N415k daga wata matashiyar mata

Mahaifiyar Elie ta ce Ubangiji ya amshi addu’ar ta na ba ta shi da ya yi bayan yaran ta 5 duk sun rasu, kuma ba ta kunyar nuna shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel