Deliget din PDP ya sadaukar da dukkan kudin da ya samu ga al'ummarsa, ya biya wa yara kudin makaranta

Deliget din PDP ya sadaukar da dukkan kudin da ya samu ga al'ummarsa, ya biya wa yara kudin makaranta

  • Wani deliget na jam'iyyar PDP mai suna Tanko Rossi Sabo, wanda ya samu makuden kudade a zaben fida gwani ya yi abun mamaki
  • An tabbatar da cewa Tanko ya tattara kudaden da suka haura miliyan 7 ya sadaukar da su ga al'ummarsa da marasa galihu a yankin
  • Ya gwangwaje kungiyoyin taimako da tallafin kudi inda ya biya wa yaran talakawa kudin makaranta da sutturu

Kaduna - Tanko Rossi Sabo, deliget din jam'iyyar PDP wanda ya koma gida da kudi makudai ya raba wa al'ummarsa tarin dukiyar a karamar hukumar Sanga ta jihar Kaduna.

Kamar yadda mai bada shawara na musamman ga marigayi Gwamna Yakowa na jihar Kaduna, Reuben Buhari ya sanar, Sabo ya kashe naira miliyan bakwai a kan marasa galihu da karfi a al'ummarsa.

Kara karanta wannan

2023: Buhari ya lissafa sharuddan da dole 'dan takarar shugabancin kasa na APC ya cika

Deliget din PDP ya sadaukar da dukkan kudin da ya samu ga al'ummarsa, ya biya wa yara kudin makaranta
Deliget din PDP ya sadaukar da dukkan kudin da ya samu ga al'ummarsa, ya biya wa yara kudin makaranta. Hoto daga thecableng
Asali: UGC
"Ya siya riguna, ya biya kudaden makaranta da na asibiti. Ya rarrabe sauran kudin domin kungiyoyin tallafi," Buhari yace.
"Ko ma dai mene ne musun kan ya yi daidai na karbar kudin ko a'a, abinda ya kwantar min da hankali shi ne ganin yadda daruruwan mutane masu karamin karfi a al'ummarsa ke murmushi a yau. A saboda haka, ina cewa sannu da aiki Tanko," ya kara da cewa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tanko Rossi Sabo yana daga cikin deliget din jam'iyyar PDP daga jihar Kaduna wanda ya halarci taron gangamin zaben fidda gwani na jam'iyyar wanda Atiku Abubakar ya bayyana matsayin mai nasara, Vanguard ta ruwaito.

Dalilin da yasa EFCC da ICPC ba za su iya gurfanar da deliget a kotu ba

A wani labari na daban, wakilan jam'iyyu suna amfani da zabukan fidda gwani wurin samun kudade daga 'yan takara, inda wasu ke kwatanta kansu da kyawawan amare yayin da suke bayyana lokutan zabe da lokutan damammaki. Sai dai 'yan Najeriya sun nuna damuwarsu kan abunda suke gani da nau'in rashawa inda suke kira da a gurfanar da deliget din.

Kara karanta wannan

Na Yi Matuƙar Takaicin Yadda Daliget Ɗin Jihar Mu Ba Su Zaɓe Ni Ba, Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Na PDP

Daily Trust ta ruwaito cewa, a yayin jawabi wurin kaddamar da wani littafi a Abuja, tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya kwatanta wannan zabukan fidda gwanin da ake yi da abun takaici.

Jonathan ya ce, "Dukkan zabukan fidda gwanin da ake yi a fadin kasar nan abun takaici ne. Ba wannan bane abinda ya dace a doka. An lalata tsarin.
"Ba za mu iya amfani da tsarin nan wurin zaben shugaban kasa, gwamnoni, sanatoci da 'yan majalisar wakilai da sauransu.
"Tsarin ya lalace, wanda hakan ba abu bane mai kyau ga kasar mu. Amma za mu yi kokari mu cigaba."

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel