'Yan Kasuwan Igbo Suna Ta Hijira Daga Bayelsa Saboda Masu Garkuwa Sun Addabe Su, Ƙungiyar Yan Kasuwa Ta Koka

'Yan Kasuwan Igbo Suna Ta Hijira Daga Bayelsa Saboda Masu Garkuwa Sun Addabe Su, Ƙungiyar Yan Kasuwa Ta Koka

  • Kungiyar yan kasuwan Igbo na Jihar Bayelsa ta koka kan yawaitar sace mambobinta da masu garkuwa ke yi a jihar hakan yasa suka fara hijira
  • Kungiyar ta ce an sace yan kasuwan Igbo fiye da 10 daga karshen 2021 zuwa yanzu kuma jarinsu gaba daya suka biya fansa da shi
  • Kungiyar ta nemi gwamnati da jami'an tsaro su kawo musu dauki domin idan yan kasuwar suka cigaba da barin garin tattalin arzikin jihar zai tabu

Bayelsa - Kungiyar yan kasuwa na Jihar Bayelsa ta koka kan karuwar sace yan kasuwan Igbo da ake yi a jihar a watannin baya-bayan nan, tana mai cewa hakan ya tilastawa wasu barin jihar saboda tsoro.

Kungiyar ta kuma yi kira ga gwamnatin jihar da hukumomin tsaro su dauki matakan magance kallubalen tsaron a jihar don tabbatar da tsaron yan kasuwan Igbo da tsare tattalin arzikin jihar, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kashe makiyaya 4, sun sace shanaye 60 a Anambra

'Yan Kasuwan Igbo Suna Ta Hijira Daga Bayelsa Saboda Garkuwa Da Mutane, Ƙungiya Ta Koka
'Yan Kasuwan Igbo Suna Ta Tserewa Daga Bayelsa Saboda Garkuwa Da Su da Ake Yi. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da ya ke magana da Daily Trust a ranar Laraba a Yenagoa, Babban Birnin Jihar, Shugaban Phone Village, Prince Williams Eze da kuma kakakin kungiyar yan kasuwan Igbo, sun ce lamarin abin damuwa ne saboda yana barazana ga tattalin arzikin jihar.

A cewarsu, daga karshen shekarar 2021 zuwa yanzu, an yi garkuwa da fiye da manyan yan kasuwan Igbo 10 a Yenagoa an kuma karbi jarinsu a matsayin kudin fansa.

Onyegesi ya ce:

"Abin da ke faruwa ba dadi, a yanzu da muke magana, mafi yawancin fitattun yan kasuwar mu suna barin Bayelsa saboda yawaitar garkuwa da mutane, shi yasa muke kira ga gwamnati ta dauki mataki saboda idan ba hakan ba zai shafi tattalin arzikin jihar. Duk yan kasuwan cikin tsoro suke don ba su san abin da zai faru da su ba.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sace mutane da yawa, sun kona motoci a wani kazamin hari da suka kai babbar hanyar Kaduna

"Daga karshen 2021 zuwa yanzu, an sace manyan yan kasuwan Igbo da dama kuma sun biya fansa da jarinsu, muna cikin damuwa domin akwai alamar suna bin mu shago-shago ne."

Jami'in Tsaro na Ohaneze Ndigbo a Jihar Bayelsa, Kwamared Patrick Ugwu ya ce shugabannin Igbo na tattaunawa da hukumomin tsaro kan batun satar mutanen ya kuma roki gwamnati ta kawo musu dauki.

A cewarsa, yan kasuwan Igbo da dama da aka sace sun rasa jarinsu saboda biyan fansa, yana mai cewa galibinsu jarin ma bashi ne.

'Yan Sanda Sun Kai Samame Maɓuyar Masu Garkuwa, Sun Ragargajesu Sun Ceto Mutane

A wani rahoton, Yan sanda a Abuja a safiyar ranar Laraba 1 ga watan Yunin 2022, sun ceto mutane hudu daga mabuyar masu garkuwa a Dutsen Dudu a unguwar Kuje sun kuma lalata maboyar yan ta'addan.

Rundunar yan sandan ta tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ta fitar kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel