Da duminsa: 'Yan uwan fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna sun fito zanga-zanga a Abuja

Da duminsa: 'Yan uwan fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna sun fito zanga-zanga a Abuja

  • 'Yan uwan fasinjojin da 'yan ta'adda suka sace a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna sun fito zanga-zanga a Abuja
  • Wannan ne lokaci na farko da 'yan uwan wadanda ibtila'in ya fada wa suka fito zanga-zanga a babban birnin tarayya
  • Sun ce makasudin fitowarsu shi ne su yi kira ga Buhari, hafsoshin tsaro da kungiyoyin duniya da su kawo musu dauki

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT, Abuja - Iyalan fasinjojin da aka sace yayin da suke kan jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna sun balle zanga-zanga a babban birnin tarayya ta Abuja.

Wannan ne karo na farko da 'yan uwan wadanda aka sacen suka fito zanga-zanga tun bayan faruwar ibtila'in, Punch ta ruwaito.

A ranar 28 ga watan Maris din 2022, 'yan ta'adda sun kai mugun hari kan jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna kuma hakan ya yi sanadin mutuwar a kalla mutum takwas yayin da 26 suka jigata kuma aka yi garkuwa da wasu.

Kara karanta wannan

Zamfara: 'Yan ta'adda sun kai farmaki kauyuka, sun halaka tare da raunata marasa kudi

Da duminsa: 'Yan uwan fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna sun fito zanga-zanga a Abuja
Da duminsa: 'Yan uwan fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna sun fito zanga-zanga a Abuja. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

Iyalan sun ce zanga-zangar sun fito ta ne sakamakon barazanar da 'yan ta'adda suka yi na cewa za su fara halaka wadanda ke hannunsu idan har ba a cika sharuddansu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sun yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, hafsoshin tsaro da kungiyoyin duniya da su kawo musu dauki.

Karin bayani na nan tafe...

AK9Train: Miyagu sun tuntubi kakakin Sheikh Gumi, sun ba FG wa'adin kwana 7 ko su aiwatar da nufinsu

A wani labari na daban, miyagun da suka sace sama da fasinjoji 60 a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna a ranar 28 ga watan Maris, 2022 suna barazanar halaka dukkan wadanda ke hannunsu matukar gwamnatin tarayya ba ta cika sharuddansu ba, HumAngle ta rahoto.

Wannan na kunshe ne a wani sautin sakon murya wanda jaridar Desert Herald ta samu inda 'yan ta'addan suka yi magana da Tukur Mamu, mai magana da yawun Sheikh Mahmud Gumi, fitaccen malamin addinin Islama na garin Kaduna.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun saki sabon bidiyon fasinjojin jirgin Abuja-Kaduna, cikin har da dan kasar Pakistan

A tattaunawar, mai magana da yawun 'yan ta'addan ya ce lokacin da gwamnatin tarayya ta same su, sun bayyana cewa suna bukatar a saki 'ya'yansu, wadanda su takwas ne kuma daga nan sai su bayyana wadanda za su saki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel