Yan bindiga sun saki sabon bidiyon fasinjojin jirgin Abuja-Kaduna, cikin har da dan kasar Pakistan

Yan bindiga sun saki sabon bidiyon fasinjojin jirgin Abuja-Kaduna, cikin har da dan kasar Pakistan

  • Kwana daya bayan barazanar kashe mutum 62 dake hannunsu, yan bindiga sun saki sabon bidiyo
  • A bidiyon farfagandan da suka aikewa yan jaridar, sun haska mutum shida cikin wadanda suka sace
  • Yan bindigan dai sun gabatarwa gwamnatin tarayya bukatunsu kuma sun yi gargadin idan ba'a biyu musu ba zasu kashe fasinjojin

Kaduna - Yan ta'addan Ansaru da suka kai hari jirgin kasan Abuja-Kaduna a watan Maris sun sake sakin wani bidiyo na mutum shida cikin wadanda suka sace a jirgin.

A bidiyon da AriseTV ta wallafa, fasinjojin na rokon gwamnatin tarayya ta kawo musu dauki ta baiwa yan bindigan abinda suke so.

Daga cikin wadanda suka yi jawabi a bidiyon akwai dan kasar Pakistan wanda yazo aiki Najeriya.

Kara karanta wannan

Zamfara: 'Yan ta'adda sun kai farmaki kauyuka, sun halaka tare da raunata marasa kudi

Dan kasar Pakistan din mai suna Abu Zayd Muhammad yace:

"Ni ma'aikacin Jmarine ne a nan Najeriya, ni dan kasar Pakistan ne, an sacemu ne ranar 28 Maris a jirgin Abuja-Kaduna, mu 62 ne kuma halin da muke ciki babu kyau. Muna kira ka gwamnatin Najeriya da na Pakistan da sauran kasashen duniya su kawo mana dauki."

Wani daga cikin fasinjojin mai suna Muhammad Dayabu ya yi kira ga gwamnatin Kaduna, ta tarayya da kungiyoyin kare hakin bil adama su taimaka musu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sabon bidiyo
Yan bindiga sun saki sabon bidiyon fasinjojin jirgin Abuja-Kaduna, cikin har da dan kasar Pakistan Hoto: @ARISEtv
Asali: Twitter

Ku sake mana 'yayanmu dake hannunku

Yan ta'addan sun yi barazanar fara kashe wadanda suka kwashe idan gwamnatin tarayya bata saki yaransu dake hannunta ba.

Shugaban yan ta'addan, Abu Barrah, yace gwamnati ta ajiye 'yayansu a gidan marayu dake Yola.

Abu Barrah ya bayyana hakan ne ga Tukur Mamu, shugaban kamfanin jaridan Desert Herald.

Kara karanta wannan

Rayuwar dan Adam ta yi arha a Najeriya: CAN ta yi Alla-wadai da kisan Fatima da yaranta a Anambra

Ya ce idan aka saki 'yayan na su, zasu saki fasinjoji mata kadai.

Yace:

" 'Yayanmu guda 8 masu shekaru 1 - 7 na tsare a gidan marayu dake Jimeta, jihar Adamawa karkashin jagorancin hukumar Sojin Najeriya."
"Sunan 'yayanmu; Abdulrahman, Bilkisu, Usman, Ibrahim and Juwairiyyah. An kwashesu ne daga hannun matanmu a jihar Nasarawa kuma aka kaisu gidan marayu a Yola."
"Kafin mu saki fasinjojin da cigaba da aikin jirgin kasan, wajibi ne a saki 'yayanmu."

Yace idan gwamnati bata sake su ba, zasu kashe fasinjojin daya bayan daya.

Kalli bidiyon:

Asali: Legit.ng

Online view pixel