Fasto Ya Yi Ɓatanci Ga Annabi (SAW) Da Al-Kur'ani a Osun Cikin Bidiyo, MURIC Ta Yi Martani

Fasto Ya Yi Ɓatanci Ga Annabi (SAW) Da Al-Kur'ani a Osun Cikin Bidiyo, MURIC Ta Yi Martani

  • Wani fasto mai suna Akintaro Joshua Ojo a Jihar Osun ya saki bidiyo inda ya yi batanci da Annabi Muhammadu (SAW) da Al-Kurani har ma da kore samuwar Allah (SWT)
  • Faston ya yi wannan munanan kalaman ne yayin da ya ke martani bisa mutuwar Deborah Samuel Yakubu wacce aka halaka a Sokoto kan batanci ga Manzon Allah
  • Kungiyar Kare Hakkin Musulmi, MURIC, ta yi tir da kalaman faston ta kuma bukaci hukuma ta yi gaggawan kama shi da daukan matakin da ya dace a kansa don kare barkewar rikici

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Osun - Wani malamin addinin kirista, mai suna Fasto Akintaro Joshua Ojo, ya yi batanci ga Allah da Annabi Muhammadu (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) da Al-Kur'ani, rahoton Independent.

Kungiyar Kare Hakkin Musulmi (MURIC), cikin sanarwar da ta fitar ranar Asabar ta bukaci jami'an tsaro su kama Fasto Akintaro bisa sakin bidiyo, inda ya yi batanci ga Allah (SWT) da Al-Kur'ani da Annabi Muhammad (SAW) da kuma addinin islama.

Kara karanta wannan

Boka ya dirkawa matar aure ciki, rikici ya barke tsakaninsa da mijinta: Ga labarin dalla-dalla

Fasto Ya Yi Batanci Ga Annabi (SAW) Da Al-Kur'ani a Osun Cikin Bidiyo, MURIC Ta Yi Martani
Fasto Ya Zagi Ga Annabi (SAW) a Osun Cikin Bidiyo, MURIC Ta Yi Martani. Hoto: Vanguard.
Asali: Twitter

MURIC ta bakin shugabanta na Jihar Osun, Dr AbdulaAzeez Ademokoya, ta ce Fasto Akintaro yana son tunzura musulmi ne da gangan.

Faston ya yi wannan batancin ne a yayin da ya ke ta'aziyya kan rasuwar Deborah Samuel, dalibar da ake zargin an kashe ta saboda ta yi batanci ga Manzon Allah (SAW) a Jihar Sokoto.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewar MURIC, babu wani musulmi mai hankali da zai lamunci kalaman faston, wadanda za su iya tada zaune tsaye a Jihar Osun da ma yankin Kudu maso Yamma ko janyo rikicin addini.

Kalaman batancin da Faston ya yi sun yi muni matuka ta yadda Legit.ng Hausa ba za ta iya rubuta su ba.

Hakazalika, an jiyo faston na kore samuwar Allah da tsarkinsa da kuma samuwar Mala'ika Jibrilu.

Faston ya kuma rubuta lambobin wayarsa a sakon faifan bidiyon yana mai cewa a shirye yake ga duk wanda zai kai masa hari saboda maganganun da ya furta.

Kara karanta wannan

Zagin Annabi: Dole A Yi Adalci Kan Kisar Deborah Yakubu, In Ji Amina Mohammed

Ba za mu dauki doka a hannun mu ba - MURIC

Kungiyar ta MURIC ta ce ba za ta dauka doka a hannunta ba ta kuma yi kira ga daukakin musulmin Jihar Osun su bari hukuma ta dauki matakan da suka dace a kan faston.

"Yankin Kudu maso Yamma fi ko ina hadari saboda yawan musulmi da kirista da sauran mabiya addinai don haka idan rikicin addini ya barke za a yi asarar miliyoyin rayuka," in ji Dr Ademokoya.

MURIC ta yi mamakin abin da Fasto Akintaro ke nufin cimma da wannan munanan kalaman da ya furta kan Allah da Manzon Allah (SAW) da Al-Kurani mai tsarki.

Daga karshe ya yi kira ga rundunar yan sandan Osun da sauran hukumomin da abin ya shafa su dauki mataki cikin gaggawa kan faston don kauce wa tashin hankali.

Ƙungiyar CAN Za Ta Yi Gagarumin Zanga-Zanga Na Ƙasa Kan Kisar Deborah Samuel

Kara karanta wannan

Batanci ga Annabi: Gwamnati ta cire takunkumi a Sokoto, ta haramta zanga-zanga

A wani rahoton, kungiyar Kiristoci ta Najeriya, CAN, ta bukaci a yi zanga-zanga na kasa bisa kisar da aka yi wa Deborah Samuel, dalibar aji 2 na Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari da ke Sokoto, rahoton Vanguard.

Shugaban CAN, Rabaran Olasupo Ayokunle, cikin wasikar da ya aike wa dukkan shugabannin kungiyar, ya bukaci kiristoci su yi zanga-zangar lumana a harabar cocinsu a ranar Lahadi 22 ga watan Mayun 2022.

Ya yi kirar ne bayan kisa da kona wata daliba da fusatattun matasa suka yi bayan zarginta da furta kalaman batanci ga Annabi Muhammadu (SAW).

Asali: Legit.ng

Online view pixel